Jami’o’in Najeriya da Kalubalen kirkira da samar da kwararru, Ahmed Ilallah

Tabbas Nijeriya ta samu kanta a wani yanayi a cikin wannan shekaru, banda abin da ya fito a zahiri na talauchi da karayar tattalin arziki kama da bullowar ta’adanci da sunan addini a arewacin Nijeriya wanda ya haifar da kungiyoyin ta’adda irin su Boko Haram, ISWAF, kaluballe na ‘Yan-fashin Daji, Satar Mutane don biyan Kudin fansa. Wanzuwa da kungiyoyin bore irin su IPOB, Oduwa Republic, karuwar masu zamba ta hanyar internet (Fraudsters) wand yafi tasiri a kukdancin Nijeriya. Wadannan matsalolin sun dau rayukan dubban yan Nijeriya, sun sanya miliyon yan kasar rabuwa da muhallan su, sun raba iyalai da dama, rabuwa ta har abada, hakan ya kawo koma baya mutuka a wajen ilimi, kiwon lafiya da zamantakewa.

Gurbacewa da lalacewar siyasa da mulkin dimokaradiyya, bunkasa da sabon salon almundahana, cin hanci da rashawa a wannan kasar kadai, ya isa muyi karatun tanutsu, kullum Nijeriya tana cikin kasashe koma baya a duniya wajen ingantancen mulki da cigaban dimokaradiya, talauchi da koma bayan tattalin arziki, shugabanni sun gaza samar da mafita.

Musani fa ita kanta Dimokaridyyar da salon yadda ake gudanar da it bincike ne na masana da jami’io ya samar da ita, kuma kullun bibiya ake bisa ilimi na al’ummah na zahiri don kara inganta ta da kawo sauyin da ya dace da yanayin da aka samu kai.

Amma fa musani duk wadannan matsalolin magance su ya wuce kawai yin yaki ko hukunta su a gaban kuliya dole sai an bawa kwararrun mu dama sun binciko musabbabin aukuwarsu, ruruwarsu dama yadda ake kitsa su, domin ta haka ne kawai za a iya maganinsu har abada a kuma dora Nijeriya a bigiren cigaba.

Tabbas cigaban kowace kasa a duniya ya ta’allaka da kokarin kasar na cin ribar ilimin da take samarwa yan kasarta, mu samman a wannan zamanin na gudun yada kanin wani, bisa doron da cigaban kimiya da fasaha ya dora duniya a kai, musamman fasahar sadarwa ta zamani (ICT).
Jami’a dama manyan makarantu ba kawai anyi su bane don koyo da koyarwa ba ko bada kwalin digiri ko diploma ba kadai. Jami’a wurin ne na koyo da koyarwa da kuma bincike, yayin da binciken da aka gudanar, a kan shigo da shi don bunkasa rayuwar al’umma, kasa da duniya baki daya.

Duk cigaban da ake gani a duniya na kowane fanni daga kere-kere, fasahar tattalin arziki, noman zamani, zaman lafiya da dabarun yaki ana samar da sune ta hanyar bincike, wanda akasari a kan yi su a Jami’a ko manyan makarantu.

Farau din fasahar sadarwa ta zamani wato computer an kirkiro tane a Manchester University a shekarar 1948 daga kwararrun masu ilimin kimiya Freddie Williams da abokin aikin sa Tom Kilburn. Mark 1, injin da ke gani har hanji wato (scanning machine), an kirkire shine a University of Aberdeen. Magani mai yaki da cutukan bacteria wato Penicillin an fara kirkirarsa ne a University of Sheffield a 1930. Duka wannan yana daga aikin bincike da ake gudanarwa a Jami’oi da manyan makarantu.

Fasahar Web Browser da Talabijin din zamani ta Bango (Plasma Screen) an kirkira ne a University of Illinois ta kasar Amurka, haka zalika fasahar injin bincike na sadarwar zamani wato google an bincikota ne da kirkirar sa a Stanford University, wanda a yau kasafin kudin (Budget) kamfanin Google, yafi girman Kasafin kudin Nigeria. Jahar California ta kasar Amurka tana daga cikin masu karfin tattalin arziki a duniya, tana samun kudin shiga akasari daga amafanin bincike na fasaha da ga Stanford University dake jaharta ta hanyar cusa binciken cikin harkokin kasuwaci da tattalin arziki.

A duniyar yau magana ake ta artificial intelligence, robotic, block chain, biosensors, 5G da sauran su, wanda kusan da wadannan kirkiru ne ake daura kinshikin gina tattallin arzikiki da bunkasar sa. A yau kamfanin sadarwa irin su Microsft Facebook, Twitter da sauransu suna da karfin arzikin da yafi kasashen Africa da dama.

Duk wannan fasahar an kirkiro su ne bisa bincike da akeyi a Jami’oi da manyan makarantu na kasashen turai musamman ma Amurika.

Ba wai kawai bincike na zahirin kimiya ba hatta bincike na zamantakewar Dan-adam, da yadda kasa zata zauna lafiya, da yadda kasa zata bunkasa tattalin arzikinta, bincike na dabarun yaki da kare kai da duk wani fanni na rayuwar al’ummah duka a kasashen da aka ci gaba ana gudanar dasu ne a manyan makarantu da Jami’oi, wannan ya sanya dangantakar gown da town ta ke da mutukar muhimmanci a Jami’a.

Amma fa Jami’oin Nijeriya da shehunan malamai da dalibai suna cikin sukunin yin bincike da zaiyi tasiri kamar haka? Kamun ludayin da aka yi wa ilimin manyan makarantu a Nijeriya yayi munin da ba zai haifar da da mai ido ba harma ya fidda kitse da ga rogo, wannan matsalolin a zahirance suke.

ASUU da gwamnatin tarrayya dama sauran ma’aikatan Jami’a irin SSANU sun kasa kai gaci wajen samun tabbataciyar matsaya akan ilimin jami’oin, haka zalika Malaman da ma’aikatan manyan makarantun kasar nan, a wani zangon, tsawon yajin aiki da ake yi yafi lokacin karatun da ake yi, balle a samu lokacin bicike na dunbin matsalolin kasarnan.

A Nijeriya ne ake biyan Professor albashin kasa da $1,000, ga kuma jibgin aiki na koyo da koyarwa akan sa, sannan a tsammaci kyakkywan tunani a wajensa na yin bincike da kirkira. Wanda a fagen ilimi wanann albashin yayi kadan bisa yanayin tsadar rayuwar Nijeriya. Talauchi babban tasgaro ne a harkar ilimi.

Jami’oin Nijeriya suna cikin mummnan hali na rashin gine-gine na dole don koyo, koyarwa da binchike, dakin gwaje-gwaje (laboratories) abin takaici ne, kai hatta ruwan sha, wutar lantarki, wurin kwanan dalibai, dakunan daukan karatu duka suna cikin mummunan yanayi, balantana offisoshin malamai. Yunkurin ayi gyara ya sanaya ake ganin rigimar kungiyoyin nan da gwamnati ta gagara karewa.

Banda gamagarin matsalolin da suka sahafi manyan makarantun mu, shi kansa kudin da ake warewa don Binciken (Research Grant) yayi kadan mutukka. Hukumar kasa ta TETFund wanda take da alhakin tattara kudaden haraji na ilimi daga kamfanoni ke biya don rabashi ga manyan makarantu na kasa, a baya ta kan ware Naira Bilayan Uku kachal (N3B), amma wannan gwamnatin ta kara zuwa N7.5B, wanda wannan kason yayi kadan mutuka in har ana son kwalliya ta biya kudin sabulu. Tsohon shugaban hukumar jami’oi ta kasa (NUC) Professor P. Okebukola yayi nuni da cewa N7.5B yayi kadan mutuka, wannan kason da ake warewa bai kai yawan wanda ake ba kananan masu bincike ba na MIT da Harvard.

Sannin kanmu ne Allah ya yiwa Nijeriya baiwa da masu ilimi, bincike da aiki tukuru, amma samun dama da kuma kudaden yin wannan binciken duk da kasancewar wani lokacin akan samu gudunmawa da ga wasu hukumin masu zaman kansu ko kamfanoni.

Kamar yadda samun gudunmawar Bincike akwai na gida da kuma waje (wato hukumomin kasashen duniya), wanda wannan shi yafi wahalar samu a wajen malaman jami’oin misali a yan shekarun baya, wasu Malaman Jami’ar Legas (UNILAG) sun sami tallafi na bincike (Research Grant) daga hukumomin kasashen wajen kimanin N12B.

Rashin ganin tasirin bincike da manyan makarantun mu a zahirance, ke sanya shakkun yi ko ingancin binciken ko kuma rashin amfani da shugabanni basa yi akan binciken. Wai shin me ka faruwa ne a kasar mu wajen ganin tasirin irin wadannan binciken da makamantan su don raya kasarmu. Shin Shehunnnan Malaman mu a Jami’a basa kirkira ne ko bincike? Ko kuma binciken baya shigowa cikin al’umma? A’a shugabannin kasarne ba sa bawa wannan bangare muhinmanci?

Koda an samu amsoshin wadannan tambayoyi, to tabbasa akwai tazara ta masu mulki da bangaren ilimi. Dalilai da dama sun nuna shugabbannin Nijeriya suna jagorancin tane ba akan doron ilimi ba, ko kuma yiwa mulkin gangancin don rashin kishin kasa ta yadda zamu bawa wannan fanni muhimmanci kamar kowace kasa mai son ci gaba a duniya.

A kullum ana kashe magudan kudade don hayar kwararru daga kasashen ketere, wanda za’a iya samar da su a gida, in har an inganta koyo, koyarwa da bincike a manyan makarantun mu. Duk dinbin jami’oin mu, har yanzu bamu daina shigo da irin shukawa a gona ba, bamu daina shigo kayan da zamu iya ganoshi da ingantashi a kasar mu ba.

Duk kasar da ta kasa bincike da samo maslaha kan al’amuran cigabanta da matsalolin dake damun al’umarta, tabbas an barta a baya, kuma talauchi zaichi gaba da mata kawanya tunda babu dabaru na ilimi wajen yaye wannan matsaloli.

[email protected]