Jami’ar Maryam Abacha, MAAUN ta saka wa ginin jami’ar sunan marigayiya Magajiya Ɗanbatta

Shugaban jami’ar Maryam Abacha dake Nijar da Najeriya da kuma jami’ar Franc-British University dake Kaduna Farfesa Adamu Gwarzo ya sanar da raɗawa ginin sashen koyar aikin Shari’a na jami’ar sunan marigayiya Magajiya Ɗanbatta.

Allah yayi wa marigayiya Magajiya Ɗanbatta rasuwa ranar Juma’a bayannfama da ta yi da ƴar gajeruwar rashin lafiya da ta yi fama da shi.

Magajiya ta rasu ranar Juma’a asibiti a Kano.

A sakon ta’aziyyar da ya aika wa iyalai da ƴan uwan Marigayiyar, Farfesa Gwarzo ya bayyana cewa ko shakka babu an yi rashi a ƙasar nan musamman a yankin Arewa.

” Baya ga wannan suna da muka raɗa wa ginin sashen koyon aikin Shari’a zamu karramata da lambar girma na Dakta.

Idan ba a manta ba, Ɗanbatta ta yi fama da kamin talauci da yayi sanadiyyar makancewarta.

Daga baya shugaban jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar ya kirkiro da ƴar kwaryakwaryar gidauniya don a taimaka mata.

An tara kuɗi masu yawa wanda aka je har garin Makoda jihar Kano aka gina mata gida aka gyara mata sannan aka kaita asibiti.

Farfesa Adamu Gwarzo na daga cikin waɗanda suka yi namijin ƙokari wajen bada kyauta mai tsoka a wannan tallafi ta aka tara wa marigayiyar.

Akarshe yayi datan Allah ya sa Aljanna ce makomarta, Amin.