INUWA BA KI ƘYAMAR KOWA: APC ta tsaida Andy Uba dan takarar gwamnan Anambra

Yayi da jam’iyyar APC ta buɗe ƙofa tsoffin kuraye na tururuwa a cikin jam’iyyar, a yanzu haka tuni jam’iyyar mai mulkin Najeriya ta bai wa tantirin ɗan duniya Andy Uba takarar gwamnan Jihar Anambra a zaɓen da za a yi nan da watanni biyu a cikin Nuwamba.

Andy Uba sananne ne ba a Najeriya har a ƙasashen waje, musamman Amurka inda ya taɓa zama, sai kuma Birtaniya, ƙasashe biyun da ya tula masu kashi mai ɗoyin mummunar harƙallar da su ka fatattake shi.

A Ingila dai an haramta masa shiga ƙasar, saboda ya tafka laifin da mahukuntan ƙasar su ka ce “ba shi ɗabi’ar mutanen kirkin da har za a yi mu’amala da shi a ƙasar.”

Idan ba a manta ba, Andy Uba ya taɓa tsayawa takarar gwamnan Jihar Anambra, har ya ci zaɓe a cikin 2007. Amma kuma Kotun Ƙoli ta soke zaɓen sa, bisa hujjar cewa Gwamna Peter Obi na lokacin bai cika wa’adin sa a kan mulki ba.

A wancan lokacin dai Andy Uba ya fito takara ne a ƙarƙashin PDP.

A Amurka an kama Andy Uba da kuɗi dala 170,000 cikin 2003, waɗanda ya yi sumogal a cikin jirgin Shugaban Ƙasa, a lokacin da su ka raka Olusegun Obasanjo halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Jami’an Amurka sun tuhume shi da laifin ƙin bayyana kuɗaɗen a Filin Jirgin JF Kennedy da ke New York.

Bayan sun ƙwace kuɗaɗen waɗanda ya rigaya ya damƙa wa wata farkar sa mai suna Lauretta Mabinton, sun kuma ƙwace wata dalleliyar Marsandi SL500, wadda Lauretta ta saya dala 91,262.50 da ta ke shirin aiko wa Andy Uba da ita a Najeriya.

Irin yadda Andy Uba ya samu karɓa a Fadar Shugaban Ƙasa da kuma a hannun manyan ‘yan siyasar Anambra, zai yi wahala a ce bai lashe zaɓen gwamna a Jihar Anambra ba.

Idan hakan ta tabbata, APC ta damƙa Jihar Anambra a hannun gogarman harƙallar 419 kenan.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi azarɓaɓin karɓar Femi Fani-Kayode zuwa APC a Fadar Shugaban Ƙasa, tun ma kafin ya yanki rajistar shiga jam’iyya a mazaɓar ƙauyen su.