INEC ta dage zabe a rumfuna 10 a jihar Legas

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage zaben gwamna da na majalisar dokokin jihar amazaɓun Victoria Garden City dake jihar Legas a ranar Asabar.
Jami’in hukumar INEC Segun Agbaje ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai ranar Asabar.
Agbaje ya ce hukumar ta dage zabe a Victoria Garden City a rumfunar zabe 10 masu yawan mutane 5,624 dake da rajista da waɗannan rumfunar zaɓe.
Dalilin yin haka inji INEC shine don a canja wa mutanen dake zama a wannan rukunin gidaje na VGC saboda matsala da aka samu.
Sai dai sun ki amincewa da sabon tsarin INEC din, dalilin haka yasa a ka dage zaɓen zuwa ranar Lahadi da safen.