INEC ta ƙara inganci, yanzu maguɗi ba zai yi tasiri ba -Shugaban CAN

Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Jihar Filato, Polycarp Lubo, ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), inda ya ce a yanzu hukumar ta inganta, kuma ta kamo hanyar zama sahihiya abin dogaro a batun zaɓe.

Da ya jawabi wani taron Mabiya Ɗariƙar Katoliƙa na Pankshin da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kanke, Lubo ya ce yanzu dai INEC ta inganta, kuma maguɗi ya ragu sosai a wurin zaɓe.

Sannan kuma ya yi kira ga Kiristoci cewa kowa ya tashi ya mallaki katin rajistar zaɓe, domin a zaɓi mutane nagari a kan mulki.

CAN ta zaburar da Kiristoci su tashi su mallaki katin zaɓe, don huce takaici.

Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN), Reshen Jihar Filato, ya jaddada wa Kiristoci cewa hanya ɗaya sa a yanzu za su samu shugabanni nagari, ita ce su tashi su mallaki katin zaɓe, domin zaɓen nagari a kan muƙamai daban-daban.

Polycarp Libo ya yi wannan kira ne a lokacin taron laccar Mabiya Ɗariƙar Katoliƙa na Pankshin da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kanke, cikin Jihar Filato, a ranar Lahadi.

Da ya ke jawabi wurin taron mai taken “Hanyoyin Dacen Samun Gwamnati Tagari, Zaman Lafiya da Ci Gaban Ƙasa”, Lubo wanda babban Rabaran ne ya ce “mallakar katin zaɓe ne kaɗai hanyar da Kiristoci za su bi domin su zaɓi shugabannin ƙwarai kuma nagari.

“Yanzu Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ƙara gyaruwa, ta kuma ƙara inganci. Irin yawan maguɗin zaɓen da aka riƙa yi a baya, yanzu duk ya ragu sosai.

“Sannan kuma samuwar wannan Sabuwar Dokar Zaɓe da aka sa wa hannu zai ƙara canja abubuwa da dama.

“Saboda haka ƙuri’un ku su ne makaman ku, kuma su ne ƙarfin ku na samun shugabanni nagari.

“A da ne ake cewa ƙuri’a ba ta da wani tasiri. Amma a yanzu dai ƙuri’a ce ke da tasiri, ba maguɗi ba.”

Rabaran Fada Libo ya kuma yi wa Kiristocin da ke kan muƙamai daban-daban na mulki cewa su ji tsoron Ubangiji, su yi gaskiya da kuma riƙe amanar da aka ba su.