INEC ba za ta rufe rajistar zaɓen 2023 a ƙarshen Yuni ba – Farfesa Yakubu

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba za a rufe rajistar zaɓe ba har sai hukumar ta gamsu da cewa jama’a sun yi amfani da damar ƙarin wa’adin da za ta yi, sun yi rajista sosai.
Yakubu ya ce saboda haka mutane su kwantar da hankulan su, INEC ba za ta rufe yin rajistar zaɓe ba a ranar 30 Ga Yuni, 2022.
Shugaban na INEC ya yi wannan albishir ɗin ne yayin da ya ke wa dandazon matasa jawabi a Tsohon Dandalin Fareti a Abuja.
Matasan dai sun taru ne domin halartar gangamin wayar wa matsala kai kan muhimmancin yin rajista.
INEC ce ta shirya gangamin tare da haɗin-guiwar ƙungiyar bin diddigin zaɓe ta ‘Yiaga Africa’, kuma Ƙungiyar Tarayyar Turai ce ta ɗauki nauyin shirya taron.
A jawabin sa da ya ke yi a ranar Asabar, Yakubu ya ce, “Ku na so ku sani ko INEC za ta rufe yin rajista nan da kwanaki biyar?
“To a madadin INEC ina tabbatar maku cewa ba za a rufe rajista ba, har sai mun gamsu da cewa yawan jama’ar da mu ke son ganin sun mallaki rajistar zaɓe duk sun samu dama sun yi rajista.”
Yakubu ya ce nan ba da daɗewa ba INEC za ta fitar ranar da za daina rajista.”
Yayin da ya ke ƙarin haske kan ci gaban da ake samu wajen ci gaba da rajista, Yakubu ya ce a cikin kwanaki biyar cakal da ake rajista a cikin Tsohon Filin Fareti, an yi wa mutum fiye da 14,000 rajista.
INEC Za Ta Ƙara Yawan Na’urar Rajistar Zaɓe A Kowace Jiha -Farfesa Yakubu:
Shugaban INEC Mahmood Yakubu ya jaddada cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa za ta ƙara yawan na’urorin rajistar zaɓe a dukkan jihohin ƙasar nan.
Ya ce INEC za ta ƙara wa’adin yin rajista domin tabbatar da cewa hukumar ta bai wa ɗimbin ‘yan Najeriya isasshen lokacin yin rajista, ta yadda jama’a da dama za su samu jefa ƙuri’a a zaɓen 2023.
“Mun raba ƙarin na’urorin yin rajista zuwa jihohi a wannan makon, kuma yanzu ma za a ƙara aikawa da su a wasu wuraren tsakanin Litinin zuwa Juma’a.” Inji Yakubu.
Da ya ke amsa jinjinar da dandazon matasa su ka riƙa yi, su na cewa, “ba ma son maguɗin zaɓe”, Yakubu ya tabbatar masu cewa, “zaɓen Gwamnan Jihar Ekiti da aka yi makon jiya ya yi kyau. Na Gwamnan Jihar Osun da za a yi nan gaba zai fi na Osun kyau. Shi kuma zaɓen 2023 zai fi kowane sahihanci.”
A jawabin sa, Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS Samuel Isipi, ya yi kira ga ‘yan Najeriya kada su riƙa sayar da ƙuri’un su ga ‘yan siyasa.