INA MAI SON TUKUICIN NAIRA MILIYAN 3?: Rundunar Tsaron Najeriya na neman Turji, Kachalla, Halilu Sububu da wasu ‘yan ta’adda 15

Rundunar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta buga fastar cigiyar wasu riƙaƙƙun ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane su 19, waɗanda ta ce ta na farauta ruwa-jallo.
Ciki wata sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya, Jimmy Akpor ya ce akwai lada ko rikuicin naira miliyan 3 ga duk wanda ya bada labarin da ya yi sanadiyar kama ɗaya daga cikin kowane ‘yan bindigar 19.
Ya ce waɗanda ake cigiya ɗin su ne su ka addabi jihar Zamfara da kisa, fashi da garkuwa.
Cikin waɗanda ake neman kuma aka buga fastar hotunan su, akwai Bello Turji, Sani Ɗangote, Leko, Dogo Nahali, Halilu Sububu, Nagoma da Nasanda.
Sauran sun haɗa da Ali Kachalla, Abu Raɗɗe, Ɗanɗa, Sani, Umaru Ɗan Hajiya, Isiya Kwashen Garwa, Alhaji Ado Aliero da Monore.
Akwai kuma Gwaska Ɗanƙarami, Ɓaleri, Mamudu da Nagala.
Sanarwar ta ce duk wani mai ƙarin bayanin yadda za a damƙe ɗayan su to ya buga lambar wayar nan: 09135904467.