ILLAR ƁARAYIN GWAMNATI: Hukumomin yaƙi da rashawa sun ƙwato naira biliyan 900 cikin shekaru 20 -Cewar CDD

Hukumomin Yaƙi Da Rashawa uku da su ka haɗa da EFCC, ICPC da CCB sun ƙwato kuɗaɗe da kadarorin da su ka kai naira bikiyan 900, kwatankwacin dala biliyan 2.26.

Cibiyar Bunƙasa Nagartar Dimokraɗiyya (CDD) ce ta bayyana haka, a cikin wata takardar da ta fitar mai taken “Ayyukan Shekaru 20 Na Ƙungiyoyin Yaƙi Da Rashawa.”

CCB ta ce an samu nasarar ƙwato yawancin kuɗaɗen da kadarorin ne ta hanyar tsarin ƙwatar kuɗaɗe da kadarorin gwamnati na “Ƙwatar Kuɗaɗe Asiri Rufe”, ‘wato plea bargain repayment’ da kuma tsarin ƙwace makudan kuɗaɗe da kadarorin da mai su ya ƙi ko ya kasa gabatar da gamsasshiyar hujjar yadda ya same su bisa ka’idar doka.

CCD ta ƙara da cewa tsare-tsaren yaƙi da cin hanci da rashawa wanda gwamnatin Buhari ta shigo da shi, ya taimaka ƙwarai da gaske wajen ƙwato haƙƙin jama’a daga hannun gaggan ɓarayin gwamnati.

CCP ta ci gaba da cewa tsakanin shekarun 2010 zuwa 2020, EFCC kaɗai ta gurfanar da mutum 3,362, kuma tuni aka yanke masu hukunci.

Sai dai cibiyar ba ta bayyana adadin yawan mutanen da ICPC ko CCB su ka gurfanar a kotu ba.

A gefe ɗaya kuma, CCD ta nuna matuƙar damuwa bisa yadda ake barin kadarorin da aka ƙwato su ke lalacewa ko salwanta daga hannun hukuma.

Yayin da ake ƙorafin zargin salwanta wasu kadarorin da aka ƙwato, makonni biyu da su ka gabata ne dai Minista Malami ya kafa kwamitin binciko waɗanda ake zargi sun fara sayar da kadarorin da aka ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kafa Kwamitin Bankaɗo Waɗanda Su Ka Fara Sayar Da Kadarorin Gwamnatin Tarayya, waɗanda aka ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati.

Kafa kwamitin ya biyo bayan ɓullar wasu rahotanni a jaridu da su ka ce wasu a cikin Ma’aikatar Harkokin Shari’a sun fara sayar da kadarorin da gwamnatin ta ƙwato a ɓoye ta ƙarƙashin ƙasa.

Cikin wata takardar da Kakakin Malami ya raba wa manema labarai a ranar Talata, ya ce, “Ministan Shari’a Abubakar Malami bai bada iznin a fara sayar da kadarorin ba. Kuma idan ma har wasu sun aikata laifin sayar da wasu daga cikin kadarorin, to ba da iznin sa ba.”

Gwandu ya ce a kan haka Malami ya kafa Kwamitin Mutum 5, da za su binciko tare da gano waɗanda ke da hannu wajen sayar da kadarorin, idan har an sayar da wasu ɗin.”

Kwamitin na ƙarƙashin shugabancin Daraktan Shigar Da Ƙararraki na Tarayya (DPP), sai kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Shari’a a matsayin sakataren kwamiti.

An bayar da mako ɗaya duk mai wata hujja ko ƙarin haske kan wannan zargi, to ya gaggauta aikatawa a Ofishin DPP ko Ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a, daga ranar 1 Ga Disamba zuwa 7 Ga Disamba.

“Kwamiti zai bincika ya gano idan har an fara sayar da kadarorin ta ƙarƙashin ƙasa.

“Idan ya gano an fara, to zai bankaɗo duk wani ko wasu masu hannu a cikin wannan harƙalla.

“Kadarorin da za’a yi binciken a kan su, sun haɗa da gidaje, maka-makan filaye, motocin alfarma, tankokin jiragen ruwa na ɗaukar dakon fetur, masana’antu da manyan injinan sarrafa kayayyaki a cikin masana’antun da gwamnati ta ƙwace.

Biri Ya Yi Kama Da Mutum:

Majalisar Tarayya na neman ba’asin yadda aka yi da kadarorin da aka ƙwato daga tsoffin shugabanni.

Majalisar Tarayya ta nuna damuwa dangane da rashin sanin haƙiƙanin yadda aka yi da kadarorin da aka ƙwato daga tsoffin shugabannin ƙasar nan.

Kwamitin Lura da Kadarorin Gwamnantin Tarayya ne ya bayyana haka a lokacin da Babban Sakataren Kwamitin Ƙwato Kadarorin Gwamnanti a Hannun Ɓarayin Gwamnati (PIC), Bala Samid ya bayyana a gaban kwamitin a ranar Litinin.

Shugaban Kwamitin Majalisa Honorabul Ademorin Kuye, ya bayyana cewa sun gano cewa wasu kadarorin da aka ce an sayar, to ba a sayar da su ba.

Kuma kwamiti ya gano wasu gidajen da aka sayar ɗin har yanzu ba a biya kuɗaɗen ba.

Musamman kwamitin ya nemi a kawo masa bayanai dalla-dalla dangane da yadda aka yi da kadarori ko kuɗaɗen da aka karɓo waɗanda tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya kimshe a ƙasashen waje, sai daga baya lokacin wannan gwamnatin aka riƙa maido kuɗaɗen.

Kuye ya kuma ɗora alamomin tambaya akan yadda aka sayar da wasu kadarorin.

Ya ce sun gano har yanzu wasu akwai jama’a a ciki, ba su fita ba, alhali an shaida masu cewa gidajen babu kowa a cikin su.

Kwamiti ya kuma nemi sanin adadin kuɗaɗen da aka sayar da kadarorin, tare da gabatar masa da shaidar ko nawa aka saka a aljihun gwamnatin tarayya.

Babban Sakataren Kwamiti Bala Samid ya ce gidajen da har yanzu mazaunan su ba su tashi ba, sun kasa biyan haya ne, kuma a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin fitar da su, sai su je kotu su samu umarnin hana fitar da su da tsiya daga kotuna daban-daban.

Ya ce ya na maraba da duk wani mataki da Majalisar Tarayya za ta ɗauka, domin a karɓo kuɗaɗen hayar da mazauna gidan su ka ki su biya.