ILIMI YA SHIGA GARARI: An ƙara kuɗin WAEC kuma an riƙe jarabawar ɗaliban da ake bin jihohin su bashin kuɗin jarabawa

Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare (WAEC), ta ƙara kuɗin jarabawa daga naira 13,950 zuwa naira 18,000.
Kenan an yi ƙarin kashi 29 bisa 100 na kuɗin jarabawar fita sakandare kenan.
Ƙarin zai fara ne daga kan ɗaliban da za su yi jarabawar SSCE cikin shekarar 2022 mai kamawa nan da watanni biyu.
WAEC ta yi wannan sanarwa ce a ranar Litinin a Legas, lokacin da ake bayyana sakamakon jarabawar SSCE (May/June).
Wanann sanarwar ƙari ta zo ne tare da sanarwar cewa babu wani ɗaliban da zai ga sakamakon jarabawar sa, matsawar dai ana bin gwamnatin jihar sa bashin kudin jarabawa amma ba a biya ba.
Shugaban Ofishin WAEC da ke Najeriya, Patrick Aregham ne ya yi wannan sanarwa, wanda ya ce dalilin ƙarin sun haɗa da annobar korona, tsadar rayuwa da kuma matsalar tsaro.
Areghan ya ce duk makarantar da ta caji sama da naira 18,000, aljihun su za su zuba kuɗin, ba ga ofishin WAEC ba.
Sai dai Areghan bai bayyana sunayen jihohin da gwammonin su ba su biya wa ɗaliban kuɗin WAEC ɗin ba. Amma ya ce ba za su saki jarabawar duk wani da ake bin jihohin da ya fito bashin kuɗin jarabawar WAEC.
Mutum sama da miliyan 1,274,784 sun ci jarabawar WAEC
Hukumar Shirya Jarabawar WAEC ta ce daga cikin mutum 1,560,261 da su ka zauna jarabawar ta WAEC ta ce kashi 81.7 duk sun ci darurra biyar da su ka haɗa da Lissafi da Turanci.