IDAN KURA NA MAGANIN ZAWO…: PDP ta ce APC ta ji da matsalolin da ke jikin Tinubu, ta daina magana kan rikicin rundunar ATIKU 2023

Jam’iyyar PDP ta sake mayar wa APC raddi mai raɗaɗi, bayan Kakakin Kamfen ɗin APC, Bayo Onanuga ya yi wa PDP da ɗan takarar ta Atiku Abubakar barkwanci dangane da rikicin shugabancin da ya dabaibaye rundunar kamfen ɗin Atiku da PDP baki ɗaya.
A ranar Juma’a ce dai Onanuga ya bayyana cewa ko an zaɓi Atiku Abubakar a 2023 ba zai iya yin komai a Najeriya ba, kuma ba iya haɗa kan ‘yan Najeriya ba, tunda ya kasa haɗa kan shugabannin PDP daidai lokacin da za a fara kamfen.
“Yaushe mutumin da ya kasa haɗa kan jam’iyyar sa zai iya haɗa kan Najeriya? Ai ba’a kawai ya ke yi, ba iyawa zai yi ba.
“Mutumin da ya kasa magance matsalolin da su ke a fili a cikin jam’iyyar sa, zai iya riƙe Najeriya har ya ƙara danƙon zamantakewar al’ummar ƙasar?”
Onanuga ya ce Atiku ƙara ruguza ƙasar zai yi ba haɗa kan ta ba.”
Sai dai kuma a raddin da Kakakin Kamfen ɗin Atiku Abubakar, Daniel Bwala ya mayar wa Onanuga, ya ce ai maganar da Onanuga ya yi ta yi daidai da maganin cutar da ke damun APC ba PDP ba.
Bwala ya ce APC ba da wani hoɓɓasan fitowa ta sayar da Bola Tinubu a idon ‘yan Najeriya, domin ko ta kai shi kasuwa, kwantai zai yi.
“Tinubu ci gaba ne daga Gwamnati Muhammadu Buhari wadda ta kasa wajen alƙawarin da ta yi wa ‘yan Najeriya, sai ma ƙara jefa ƙasar ciki ƙuncin rayuwa da ta yi. Ga rashin tsaro ga tsadar rayuwa.”
Haka shi ma Kakakin Yaɗa Labaran Atiku Abubakar, Paul Ibe, ya ce ai rikicin PDP batu ne na cikin gida mai nuna cewa jam’iyyar na nan garau ta na motsawa, ba kwance ta ke shirim ba.
Ya ce ya kamata APC ta yi shiru saboda ba ta da bakin magana, ganin yadda batun cancantar takardun makarantar Bila Tinubu da sauran zarge-zargen da ake yi masa har yau ba a warware su ba.
Ya ce zai ga da wane ido APC za ta kalli ‘yan Najeriya ta tallata masu Tinubu idan an fara kamfen.
Ibe ya ce ‘yan Najeriya na nan na jiran zaɓe ya zo su rama abin da APC ta yi masu ta hanyar korar ta daga mulki.