Idan aka yi sakaci Najeriya ta tarwatse, za a shafe kananan kabilun kasar nan a doron kasa – Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya yi kakkausan gargadin cewa zaman Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa shi ne mafi alheri ga kananan kabilun kasar nan.

Obasanjo ya yi wannan gargadin ne a lokacin da Kungiyar Taya Kabilar Tivi ta kai masa ziyara a Abeakuta, babban birnin Jihar Oyo.

“Idan Yarabawa su ka ce sun balle sun kafa kasar su daban, su ma kabilar Igbo da ta Hausa/Fulani kowace ta balle ta kafa kasar ta daban, to yaya sauran kananan kabilu za su yi? Ai shafe su kawai za a yi a doron kasa.’ Inji Obasanjo.

Ya ci gaba da cewa tabbas akwai korafe-korafen mayar da wasu kananan kabilu saniyar-ware. Amma wannan ba dalili ba ne na neman ballewa daga kasa.

“Ba da dadewa ba cikin 2020 mu ka yi taro da kungiyoyin kabilu daban-daban. A wurin taron babu wata kabilar da ta nuna ballewa. Don haka adalci bangarori za su nema a rika yi masu, ba wai su nemi ballewa ba.

Shugaban Kungiyar Raya Kabilar Tivi, Zackrys Guyuv ya damka wa Obasanjo takardar bayanan dukkan korafe-korafen da ya ce ke zukatan kabilar Tivi dangane da halin da kasar nan ke ciki.

Daga cikin kotafe-kotafen har da yadda yankin Tivi ya afka mummunar matsalar tsaro ta fashi, kisa, garkuwa da mutane da fadace-fadacen su da Fulani makiyaya.

Wannan gargadi na Obasanjo ya zo kwana daya bayan jigon jam’iyyar Tinubu ya yi irin wannan gargadin, inda ya ce, “Idan Najeriya ta tarwatse sai mun fi Iraqi da Sudan lalacewa”

Shi dai babban jigon jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya yi kakkausan gargadin cewa masu tayar da jiniyoyin wuya su dauki darasi daga bala’in yakin Basasa da aka yi a kasar nan a baya da kuma wasu yake-yaken da su ka kassara manya da kananan kasashe.

Da ya ke jawabi wurin taron addu’o’in Tafsirin Ramadan da aka shirya a Gidan Gwamnatin Jihar Lagos, Tinubu ya ce an shirya addu’o’in don nemar wa Lagos da Najeriya zaman lafiya.

Ya ce Allah ba zai biya wa masu son Najeriya ta tarwatse bukatun su ba. Kuma ya ce ya kamata masu neman tayar da zaune tsaye su tuna cewa har yanzu Najeriya ba ta gama fita daga bala’in Yakin Basasa ba.

“Kada Allah ya kawo tarwatsewar kasar nan, domin ni dai idan kasar nan ta tarwatse, to ba ni da wani wurin da zan koma na ci gaba da rayuwa da harkoki na.

“Ya kamata tsagerun da ke tayar da jijiyoyin wuya su sani cewa zaman mu kasa daya tare da juna shi ne mafi alheri gare mu baki daya.

“Shi yaki idan ya barke, ba a rana daya ya ke karewa ba. Zai dauki tsawon lokaci, sannan kuma za a shafe shekaru masu yawa ana cikin wulakantacciyar rayuwa.

“Idan Najeriya ta tashi lalacewa, sai ta fi kasashen Iraki da Sudan lalacewa. Kuma za ta shafe tsawon shekaru cikin halin kunci ta kaka-ni-ka-yin da babu wanda ya san ranar fita.”