Hotuna: Ganduje ya Kaddamar da dakarun Hisbah 5000

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bikin makon Hisbah wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata.

Gwamnan ya Kaddamar da dakarun Hisbah na musanman su 5700 a karkashin Jagorancin Shugaban Hukumar Hisbah na Jiha, Ustaz Muhammad Ibn Sina.

Yayin taron, Gwamna Ganduje ya kuma chanjawa jamian na Hisbah Uniform da kuma karin girma ga dukkan jami’an da suka shekara shida suna aiki.

Gwamnan ya yaba da yadda Yan Hisban suke gudanar da aikin su inda yace za’a duba yiyuwar kara musu albashi.

Yayin taron Gwamnan yana tare da Mataimakin sa, Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnati, Usman Alhaji da Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas da Dattijo Nasiru Aliko Koki da Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnati, Ali Haruna Makoda.

Saura sun hada da kwamishinoni da masu baiwa Gwamna shawara da sauran jami’an Gwamnati.