Hoton Zanga-Zangar EndSARS ne aka sa a labarin wai ‘yan Kenya sun taya ‘Yan Najeriya zanga-zangar 12 ga Yuni – Binciken DUBAWA

Zargi: Wani mai amfani da shafin twitter ya wallafa wani hoto yana zargin ‘yan Kenya sun marawa al’ummar Najeriya a zanga-zangar da ta gudanar ranar 12 ga watan Yuni 2021

Har yanzu ana cigaba da turo mana zarge-zarge mu fayyace gaskiyarsu dangane da zanga-zangar da aka yi ranar 12 ga watan Yuni, wanda ya kasance ranar tunawa da girkuwar dimokiradiya a Najeriyar. Daya daga cikin irin wadannan zarge-zargen wani labari ne a shafin Free Mdude (@_iAlen) a tiwita inda mai amfani da shafin ke zargin cewa ‘yan Kenya sun nuna goyon bayansu ga ‘yan Najeriyar da ke adawa ranar 12 ga watan Yuni. Wannan labarin na dauke da hoton wasu mutane, kowannensu rike da tutar Najeriya.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da neman adireshin wanda ya wallafa wanna labarin wato Free Mdude (@_iAlen). Bayan haka sai DUBAWA ta duba ko akwai wadansu wadanda suka yi irin wannan sharhi, inda ta gano Jewel(@linaeyen) wanda shi ma ya wallafa labarin sai dai ya bayyana majiyarsa a matsayin (@_iAlen) inda aka fara ganin hoton.
Haka nan ita ma Naija PR Assistant (@starblog3a1) ta wallafa labarin amma ita ma hoton Free Mdude ta sanya. Daga nan ne DUBAWA ta sa hoton a shafin binciken google dan gano mafarin shi, sai ya bulla a wani labarin da Premium Times ta wallafa a watan Oktobar 2020 lokacin da aka yi zanga-zangar EndSARS.

Da aka cigaba da bincike sai aka gano cewa sunan wakilin Premium Times Kabir Yusuf ne a kan hoton a matsayin wanda ya dauka, dan haka sai muka tuntube shi dan jin wajen da ya dauka da kuma lokacin da ya dauki hoton.

Mr. Yusuf ya tabbatar mana cewa shi ya dauki hoton a Abuja lokacin zanga-zangar EndSARS yana cewa “wannan ba haka bane, ni na dauki wannan hoton a Abuja lokacin zanga-zangar EndSARS.

A Karshe

Labarin tiwitar da ke cewa ‘yan Kenya sun nuna goyon bayansu ga ‘yan Najeriya lokacin zanga-zangar 12 ga watan Yuni, ba gaskiya ba ne domin hoton na masu zanga-zangar EndSARS ne a watan Oktoban bara.