HIMMA DAI MATA MANOMA: Yadda na baro jihar mu na dawo ƙauyen Abuja ina noman rogo, wake, gyaɗa, shinkafa da masara – Wata mai himma

Rebecca Isaac mace ce mai himmar neman na kan ta. Wannan ƙwazon ya sa ta baro harkar noman da ta fara a jihar Edo, ta koma yankin Abuja domin samun manyan gonakin da za ta bunƙasa noman ta.

Mace ce mai ‘ya’ya shida, amma fa ko namiji bai fi ta himmar noma ba.

“Ƙauyen Abuja da na dawo ina noma, na kasa samun kamfaceciyar gona mai faɗin gaske. Sai dai na riƙa karɓar aro a wurare daban-daban.

“Akwai inda na biya kuɗin aron kadada ɗaya Naira 15,000, akwai inda na karɓa na biya Naira 10,000. Akwai ma ƙananan wuraren da na ke biyan ladar aro Naira 2,000 kacal.

“Sannan ni ban shiga wata ƙungiyar manoma ko kungiyar mata manoma ko ɗaya ba, saboda ba ni da kuɗin shiga yin rajistar wata ƙungiya. A yanzu ƙoƙari na ke yi na ga na tsaya ƙyam da ƙafafuwa na.

“Saboda matsalar kuɗi yawancin kayan harkokin noman nan duk bashi na ke karɓa. Musamman sinadaran kashe ƙwari, har shi kan sa noman ma wasu lokuta a bashi a ke yi min. Sai na samu kuɗi sannan zan biya leburorin. Idan kuɗi bai zo da wuri ba, sai su haƙura sai na yi girbi na sayar da kayan gonar tukunna.

“To idan na ɗebe kayan gona, zan tattara waɗanda ke bi na bashi. Wanda ke son kuɗi, idan na sayar sai na biya shi. Wanda ke buƙatar kayan abinci kuwa, sai mu yi lissafi na ɗibar masa.” Inji Rebecca, a tattaunawar da ta yi da PREMIUM TIMES.

“Akwai sauƙi sosai wajen yi min ayyukan leburanci bashi a gonaki na. Ko kwanan nan ma Ni da miji na mun karɓo bashin maganin kashe ƙwari. Yanzu haka ma akwai cikon Naira 6,000 ban kai ga biya ba.

“A ɓangaren rogo, na samu alheri sosai da wani ya kawo min irin rogo daga ƙasar Malaysia. Kuma cikin watanni shiga ya ƙosa har aka cire aka samu riba sosai.

“Amma sauran irin su wake, shinkafa, masara da na ke shukawa kuwa, ina tanadar iri ne da zan shuka a damina mai zuwa, daga abin da da noma a wannan kakar. Idan sun ƙare kuwa, sai na je kasuwa na sayo.”

Da aka tambaye ta batun matsalar tsoro kuwa, Rebecca ta nuna irin yadda makiyaya ke sa ta asara mai yawa.

“Ba sau ɗaya ba, kuma ba sau biyu ba na sha fama da makiyaya. Za su zo da shanu idan mu na gona, mu yi ta cacar-baki da su. Idan ba mu nan kuma su yi ɓarna su yi gaba.

“Ranar wata Lahadi na je coci na dawo na samu shanu sun cinye shinkafar da na shuka kakaf. Haushi da takaici ya kama ni sosai, ko tsayawa na lissafa adadin kuɗaɗen da na yi asara ban yi ba.

Yadda Ƙabilun Yankin Abuja Ke Nuna Min Ƙabilanci A Harkar Noma:

“Gaskiya ana nuna min bambanci da ƙabilanci sosai. Ana kuma jin haushi na musamman idan amfanin gona ta ya fi na su yabanya.

“Kai, akwai fa lokacin da na karɓi wata gona aro na biya kuɗi. Na yi shuka ta yi yabanya, har an yi noma. To sai wanda ya ba shi aron gonar ya mutu. Kawai sai ‘ya’yan sa su ka ce kada na kuskura na sake shiga gonar, duk da ni ke da amfanin gonar da ke ciki.

“To idan kuma su ka ba ka aron gona ka biya, idan ka yi shuka ka yi noma ka fi su samun yabanya da amfanin gona, idan shekarar ta dawo ba za su sake ba ka aron gonar ba.

“Kuma ni yawanci ribar da na ke samu a noma ta na tafiya ne wajen hidimar gida, kamar kuɗin makarantar yara. Ina da ‘ya’ya a yanzu haka da ke karatun digiri na farko a jami’a. Duk kuɗin makarantar su a gona ake samun su. Kuma ina da ɗiya ta yanzu haka da ke noma a Sapele.”