Haka kawai ban san hawa ba, ban san sauka ba wasu suka kantara min ƙazafi a Soshiyal Midiya – Ribadu

Tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu, ya dora alhakin mafi yawan kalubalen da kasar ke fama da a kan labaran ƙarya da kafofin sada zumunta ke yaɗawa.

Ribadu ya fadi haka ne ranar Lahadi a Abuja, yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana zargin wasu manyan jami’an gwamnati da daukar nauyin ƴan bindiga a kasar.

Tsohon shugaban na EFCC, wanda ya yi magana a wani taron manema labarai, ya ce lokaci ya yi da ya kamata ya wanke kan sa kan wannan batu, wanda ya ce an kwana biyu ana yin ta.

” A watan Yuni ne na fara cin kara da wannan sako da ka yi min ƙazafin wai daga ni ya fito. Nan take na fito na ƙaryata sakon cewa ƙage aka yi min amma ni banta ɓa aika sako irin haka, karya ne, ban sanda da wannan saƙo ba.

” Wannan mafanar banza ne, ƙage, sharri da hassada, hatta wannan rubutu ma algungumin da ya rubuta bai rubuta da kyau ba, ko turancin ma bai kware a cikin sa, ba zai yiwu irin wannan rubuta da maganar banza ya fito daga gareni ba.

” Kuma na maida martani da kakkausar murya wanda yasa dole na fito da takardar nesanta kaina daga wannan zargi.

” Na yi zaton shikenan an binne maganar , sai kuma ga shi an sake dawo wa da ita, an sake fara yayaɗata. Abin ya na baƙanta min rai matuƙa kuma ya dame ni.

Ribadu ya ce mutane da yawa sun riƙa neman sa ba a Najeriya ba har daga kasashen waje domin neman su san mene ne gaskiyar magana game da wannan sako da ake ta yayaɗawa a kafafen sada zumunta.

Amma haka yake hakuri ya yi musu bayani akai cewa ƙage ne.

” Ina so in sake faɗi a nan cewa babu abinda ya haɗani da wannan sako, ƙage ne da sharrin masharranta da basu so su ga ana zaman lafiya, dole sai an kirkiro wani abinda za ayi ta cecekuce akai. Amma tsakani da Allah hakan bai dace kuma waɗanda suka yi haka ba su yi min adalci ba, don ban faɗi ba kuma ban sanda shi ba.

” Zunibi ne babba haka kawai mutum ya kirkiri wani abu ya jingina wa wanda bai ji ba bai gani bai kuma sani ba haka kawai don yi masa sharri. Babu abinda ya haɗani da wannan saƙo.

” Wannan shine maganata da zan yi game da wannan sako da ake yaɗawa, ba daga gareni bane, ba gaskiya bane kuma ban san daga inda ya fito ba. Duk wanda ya ci karo da sakon yayi watsi da shi, ba gaskiya bane.

Ribadu ya ce tuni ya mika kukan sa ga jami’an tsaro domin a san da maganar sannan kuma idan akwai yiwuwar su nemi bin diddigin abin domin kamo waɗanda ke yaɗa wannan sako a yanar gizo.

” Kafafen yaɗa labarai na zamani wato Soshiyal Midiya, sun bada gudunwa matuka wajen jefa kasar nan a halin da muka tsinci kan mu yanzu. Ana amfani dasu ana yaɗa labarun karerayi waɗanda ke tada zaune tsaye a tsakanin mu da kawo rarrabuwar kawuna, ta hanyar amfani da addini ko kabilanci.

” Abinda ake yi ba a kyauta ba saboda haka dole gwamnati ta ɗauki mataki a kai.

” A matsayin mu na ƴan ƙasa, akwai inda karfin ka zai kare ba amma gwamnati na da dama ta ɗauki mataki akan irin waɗanan abubuwa.

Sanna kuma yayi kira ga masu mallakin shafukan sada zumunta a yanar gizo da su rika hana wa da hukunta masu amfani da shafukan suna yin izgilanci da kalaman ɓaranci ga waɗanda ba su ji ba basu gani ba.

Yace iri haka ne ya kawo tashin kalin da aka rasa rayuka Rwanda, Sereleone,da Liberia, a rika yaɗa ƙarya haka kawai don wasu basu son zaman lafiya.

” Duk da ni mutum ne mai rajin a baiwa kowa ƴancin tofa albarkacin bakinsa akan kowani abu, amma kuma kada a wuce gona da iri. A rika faɗin abinda ya dace ba ƙazafi, ƙage ko sharri ba.