Gwamnonin Kudu 17 sun saka dokar hana kiwo a jihohin su

Gwamnonin kudancin Najeriya 17 sun saka dokar hana kiwo a fili a duka fahin jihohin su 17.
Wannan matsayi da suka dauka ya biyo bayan ganawa da gwamnonin suka yi ne a garin Asaba, babbar birnin jihar Delta.
Idan ba a manta ba gwamnonin yankin kudu sun dade suna zaman doya da manja tsakanin su da fulani makiyaya.
Suna zargin Fulani makiyaya da tada zaune tsaye a jihohin na su sannan kuma da yin ikirarin sune ke ruruta rashin zaman lafiya a jihohin su musamman tsakanin makiyaya da manoma.