Gwamnatin Sokoto ta tabbatar da kisar gillar da ‘yan bindiga suka yi wa masu cin Kasuwa a Goroyo

A kasuwan Goronyo jihar Sokoto dake ci mako-mako ne ‘yan bindiga suka buda wa mutane wuta inda suka kashe mutum sama da 30 sannan da dama sun ji rauni.

Wannan hari ya auku ne kwanaki 12 da wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane a kasuwar Unguwar Lalle dake karamar hukumar Sabon Birni.

A jihar Sokoto kananan hukumomin Goronyo, Isa, Sabon Birni da Raba wurare ne da ‘yan bindiga suka addaba da hare-hare.

Wani dake kare rajin dan Adam a jihar Sokoto Basharu Guyawa ya ce maharan d suka kau su akalla 200 sai da suka zagaye kasuwar sannan suka bude wa mutane wuta ta ko ina.

Ya ce ‘yan bindigan sun dauki awowi suna barin wuta a kasuwar, ba a dai iya fayyace ko mutum naya suka sheka lahira a dalilin wannan hari ba, saidai an kiyasta cewa an ga gawarwaki sama da 30 wanda aka kashe nan take.

Wani mazaunin garin kuma tsohon ma’aikacin gwamnati Bashir Adamu ya ce ba za su taba manta wa da wannan rana ta Lahadi ba.

Ya ce maharan sun kashe mutum sama da 30 sannan mutum 20 sun ji rauni.

A ziyarar jaje da babban ahfsan sojojin Najeriya Faruk Yahaya ya kai wa gwamnan Sokoto ranar Litinin, ya tabbatar wa gwamna AMinu Tambuwal cewa za a ci gaba da suburbudar yan bindigan a lo’ina suka a fadin kasar nan.

” Wannan wannan mummunar hari ne da ba shi misaltuwa da komai. Ina kira ga rundunar soji da ta turo karin jami’ai jihar domin gamawa da ‘yan bindigan da suka addabi mutanen yankin jihar.