Gwamnatin Legas ta markaɗe baburan acaɓa 482, ta kama babura 5,200 cikin watanni shida

Gwamnatin Jihar Legas ta bada sanarwar yin amfani da katafila ta murtsuke baburan ‘yan acaɓa har guda 482.

Kakakin ‘Yan Sandan Legas Adekunle Ajisebutu ne ya bayyana haka, inda ya ce an kama baburan ne a wurare daban-daban, saboda karya dokokin tuƙi da masu baburan su ka riƙa yi.

Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Legas Hakeem Odumosu ya halarci kallon yadda aka murtsuke baburan a bainar jama’a.

“An markaɗe su a gaban jama’a ne a wannan karon, saboda a baya ba a gaban jama’a ake murtsuke su ba, shi ya sa wasu ke zargin wai sayarwa mu ke yi.

Ya ce ba za a taɓa saurara wa duk wani mai babur ɗin haya da ya karya doka ba.

Ya ce a cikin watan Oktoba an kama babura 204, kuma an kama ‘yan acaɓa 50.

Idan ba a manta ba, Hukumar Kula da Tsaftace Legas ta kuma sanar da cewa tsakanin watan Janairu zuwa Yuni, an kama baburan acaɓa 5,200.

Ya yi gargaɗin cewa masu haya da babur su guji yin amfani da baburan su wajen aikata muggan laifuka.