Gwamnatin Jigawa tayi asarar naira miliyan ₦100 sanadiyar sace-sacen injinar fanfon bada ruwa na tuka-tuka

Gwamnatin Jihar Jigawa tace tayi asarar Naira miliyan ₦100 sanadiyar sace-sacen injinar fanfon tuka-tuka a shekarar data gabata ta 2020.

Kwamishinan Ruwa, Ibrahim Garba Hannun-Giwa, ya bayyanawa ƴan Jaridu cewa a fadin Jihar, a shekarar 2020 an sace fanfon tuka-tuka sama da 163 wanda hakan yana kawo cikas wajen samar da ruwan sha ga al’umma Jihar

Garba Hannun Giwa yayi Allah wadai da halin ko’in kula da wasu al’umma suke nunawa wajen rashin martaba kayan gwamnati. Yace ɓarayin sukan ɗauki tsawon awanni suna tuge injinan famfunan tuka-tuka duk da kasancewar kuwa mutanen gari na nan ba a iya kuma kama su ko gane ko su wane ne.

Hannun Giwa ya ƙara da cewa gwannati ba zata kasance a ko’ina ba, saboda haka ya zama wajibi jama’an gari da sune ke moriyar wannan abu su rika sakawa injinar ido domin kare su daga fataken dare

Yace gwannatin Muhammad Badaru ta kashe kuɗi har Naira Biliyan ₦22 cikin shekaru shida wajen samar da ruwan sha ga mutanen Jigawa.

Hannun Giwa yace gwamnati ta gyara gidajen ruwa 284 zuwa masu amfani da hasken rana (Solar) kuma ta gina sabbin gidan ruwa 437 masu amfani da hasken rana, a cikin waɗannan shekaru shida.

Kuma gwamnati ta gina fanfunan tuka-tuka 4,077 a faɗin Jihar a cikin shekaru shida da suka wuce.

Hannun Giwa ya kuma ƙara da cewa gwamnati ta gina banɗakuna (Toilet) 2,216 a makarantu da wuraren taruka na al’umma a yunƙurinta na hana yin bahaya a waje domin tsaftar mahalli da inganta ruwan sha.

Yace hukumar UNICEF ta duniya ta baiwa kananan hukumomin Jigawa 18 a cikin 27 shaidar tsaftar mahalli bayan sun daina yin sugunnu a bainar jama’a.