Gwamnatin Borno ta gargadi mutane kada su rika siyar da abincin tallafi da gwamnati ke raba musu

A cikin farkon wannan mako ne gwamnatin jihar Barno ta gargadi mutanen da ake rabawa abincin tallafi da su rika cin abinci ne maimakon saida da wasu ke yi.
Shugabancin kwamitin tallafawa mutane na jihar Borno Saina Buba ya yi kira ga mutane da gwamnati ka tallafawa da kaya da abinci da kada su rika siyar da kayan tallafin da suka karba.
Buba ya fadi haka ne a taron tallafawa talakawa 4,000 da gwamnati ta yi a kauyukan Mairi da Maimusari dake karamar hukumar Jere.
Buba wanda shine kwamishina matasa da wasanni na jihar ya kuma hori mutane da su guji bada cin hancin domin a saka sunayen su a cikin wadanda za su samu tallafin abincin da gwamnati ke badawa.
Ya ce a yi gaggawar kawo wa kwamitin karar duk wani jami’in gwamnatin da ya nemi a biya shi cin hanci domin a hukunta shi.
Buba ya ce gwamnati ta tallafa wa talakawa 4,000 inda a cikin su akwai maza 2000 da mata 2,000.
“ Mun raba wa maza buhun shinkafa mai nauyin kg 50 sannan mata mun basu naira 10,000 , siga kg 5 da zannuwa.
Kwamishinan harkokin mata na jihar Hajiya Zuwaira Gambo ta yi kira ga mata da su yi amfani da kayan tallafi da suka samu domin yin azumin Ramadan da sallan Eid-el-Fitr.
Shugaban karamar hukumar Jere Abubakar ya mika godiyar sa ga gwamnati sannan wasu da dama da suka ci moriyar kayan tallafin da suka hada da Maryam Ali, Lucy Haruna, Jummai Buba da Isaac Dogara sun mika godiyar su ga gwamnati suna masu cewa hakan da gwamnati ke yi ya nuna musu lallai wannan gwamnati na kwaunar su matuka.