Gwamnati ta umarci makarantu su fara amfani da Tsarin Ƙara wa Malamai Shekarun Ritaya

Gwamnatin Najeriya ta jaddada amincewar da ta yi kan fara amfani da Sabon Tsarin Shekarun Ritayar Malamai kan dukkan malamai baki ɗaya.
Cikin wata sanarwa mai ɗauke da umarni wadda Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya, Andrew Adejo ya sa wa hannu, ya ce babu wani iyakar yawan shekaru da aka killace kan batun ritayar malamai dangane da yawan shekaru a duniya, ko yawan daɗewa su na koyarwa.
Sanarwar ta kuma umarci waɗanda ba su son ƙara daɗewa su na aikin koyarwa, to rubuta wasiƙar sanarwar ritayar su, kamar yadda ake yi bisa ƙa’ida.
Dokar Tsarin Ritaya ta 2022 ce ta ƙara wa malaman yawan shekaru su na koyarwa. Kuma Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sa wa dokar hannu..
Dokar dai ta ce dukkan jami’an ilmi zai kasance shekaru 65 ne lokacin ritayar su, ko kuma shekaru 40 cur malami na aiki, to sai ya yi ritaya haka nan.
“Yanzu ba a keɓance wasu an ce ba za a ƙara masu tsawon lokacin yin ritayar ba. Amma duk wanda ke son yin ritaya, to sai ya rubuta ya sanar.”
Baya Ta Haihu: Ba Kowane Malami Za A Ƙara Wa Albashi Da Alawus Ba:
Ma’aikatar Ilmi ta ce sai wanda ya cancanta a yi wa ƙarin albashi da alawus kaɗai za a ƙara wa, bayan an yi gwaji an ga cancanta.
Sannan kuma wannan ƙarin wa’adin shekaru ana aiki kan malamai da jami’an ilmi kaɗai za a yi amfani da shi.