GOMA DA GOMA: Muhyi ya maka Ganduje a Kotu

Tsohon shugaban Shugaban Riƙon Hukumar Hana Cin Hanci da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, Muhyi Magaji ya maka gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a kotu yana kalubalantar tsigeshi da aka yi a matsayin shugaban hukumar.
Muhyi ya ce gwamnatin jihar bata da ikon tsige yadda ta yi domin ya saba wa dokar jihar.
Muhyi ya shigar da kara kotun sauraren kararrakin ma’aikata dake Abuja.
Dalla-Dalla: Tsakanin Gwamna Ganduje, Majalisar jihar Kano da Muhyi Magaji
1 – Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya naɗa Shugaban Riƙon Hukumar Hana Cin Hanci da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, sati ɗaya bayan dakatar da Muhuyi Magaji.
An maye Magaji da Mahmood Balarabe, wanda kafin naɗin sa shi ne Daraktan Shigar da Ƙararraki da Gurfanar da Masu Laifi a Kotu na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano.
Kakakin Yaɗa Labarai Abba Anwar ne ya yi sanarwar ga manema labarai a ranar Alhamis a Kano.
MUHYI MAGAJI: Yadda Ƙilu Ta Ja Masa Bau:
2 – Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bada sanarwar dakatar da Muhuyi Magaji, Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci na Kano.
Kwanan baya PREMIUM TIMES ta buga dambarwar da ta kunno kai tsakanin Muhuyi Magaji da Gwamnatin Jihar Kano.
Sanadiyar wannan dambarwa dai an dakatar da Muhuyi Magaji, Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci na Jihar Kano.
Sanarwar dakatar da Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji, ta biyo bayan wata wasiƙa da Akanta Janar na Jihar Kano, ya aika wa Majalisar Dokokin Jihar Kano.
A cikin wasiƙar, ya yi ƙorafin cewa Muhuyi ya ƙi karɓar sabon akanta da aka tura a hukumar, ya ce ba zai yi aiki da shi.
An dakatar da Muhuyi tsawon wata ɗaya, kuma an kafa kwamitin da zai yi bincike. Kwamitin an ba shi makonni biyu ya kammala kuma ya miƙa rahoton sa.
Muhuyi ya yi ƙaurin suna tun bayan da ya binciki zarge-zargen da Gwamnatin Ganduje ta yi wa tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, wadda daga nan rikicin tsige shi ya samo asali.
Wannan bijirewar rashin amincewa da cire akanta na hukumar aka tura wani a madadin sa, hakan na nufin shi ne dalilin dakatar da shi.
Kafofin yada labarai a Kano irin su Freedom Radio da Sahelian Times duk sun buga labarin dakatarwar.
Musabbabin Guguwar Dakatar Da Muhuyi Magaji:
3 – Kwamishinan Yaɗa Labarai Muhammad Garba ya shaida dalilin da ya sa aka daina kashe wa Hukumar Yaƙi da Rashawar Kano kuɗi.
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana raddi ga kalaman Shugaban Hukumar Hana Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji, wanda ya ce gwamnatin ta daina kashe wa hukumar kuɗi shi ya sa ya ɗauƙi ƙoƙo ya ke bara.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ya shaida wa BBC Hausa cewa matsalar rashin kuɗi da Gwamnatin Jihar Kano ke fama da ita ce ta sa gwamnantin ta daina kula da buƙatun hukumar na gaggawa da na wajibi.
Garba ya ce hukumomi da yawa da ke ƙarƙashin gwamnantin ta Kano abin ya shafa, ba hukumar da Muhuyi ke shugabanci ba.
Amma kuma ya ce duk da haka Gwamnatin Jihar Kano na bai wa hukumar duk wani goyon bayan da ta ke bukata.
Sannan kuma Garba ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa gwamnati na ƙoƙarin tsige Muhuyi daga shugabancin hukumar.
“Ita fa gwamnati za ta iya cire duk wani ma’aikacin ta, ba tare da an riƙa yayatawa, muddin buƙatar cire shi ɗin ta taso.” Inji Garba.
An kasa samun Magaji a ranar Talata, domin a ji ko gaskiya ne idan ya na binciken wata harƙalla, daƙasharama da wuru-wurun kwangilar bilyoyin kuɗaɗen da ake ganin dalilin binciken ne shi da hukumar sa su ka shiga halin ƙuncin da su ka samu kan su a yanzu.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Muhuyi, Shugaban Yaƙi da Rashawa na Kano ya zargi jami’an gwamnatin Kano na yi masa ‘barazana da katsalandan.’
Shugaban Hukumar Hana Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji, ya yi ƙoƙarin cewa ya na fuskantar barazana da katsalandan’ daga jami’an gwamnati.
Yayin da Magaji bai bayyana sunayen masu yi masa katsalandan’ ɗin ba, ya ce abin da ake yi masa ba zai dakushe kaifin ƙoƙarin da ya ke yi na gurfanar da ɓarayin gwamnati a Jihar Kano ba.
Magaji ya yi wannan kalami a shafin hukumar na Facebook
“Ƙalubale da matsin-lamba da na ke samu daga jami’an gwamnati ya yi yawa. Wasu jami’an gwamnati kallo su ke ita wannan hukuma ta gwamnati ce, don haka su a ganin su, akwai wasu abubuwan da hukumar ko da ta ga ba daidai ba ne, wai kamata ya yi wannan hukumar ta kauda kai kawai. To amma ni ba zan taɓa yi masu yadda na ke so ba, saboda ba tsoron na rasa aiki na ke yi ba.”
“Har damƙe an yi an caje ni da laifin take umarni, saboda kawai ina binciken, wani kes. Amma wannan bai sage min guyawu ba, saboda aiki na yi bakin-rai-bakin-fama.
“Ina so jami’an gwamnati su sani kuma su fahimci cewa ba kai na ne na ke yi wa aikin nan ba. Kuma ba don na azurta kai na na ke yi ba. Duk ma mai yin wannan tunanin, kan sa kawai ya ke yaudara.
“Kai ni ko a yau na bar wannan aiki a jihar Kano, dokar Najeriya ta ba mutum ‘yancin yin zama mai bincike-ƙwaƙwaf mai zaman kan sa.
“Zan iya irin wannan aiki a ko’ina a Najeriya, a matsayi na na lauya mai lasisi.” Inji shi a cikin fushi.
“Gwamnatin Kano Ba Ta Bai Wa Hukuma Ta Kuɗi”:
Saboda gwamnati ba ta bayar da kuɗaɗe ga wannan hukuma shi ya sa “na ƙaddamar da gidauniyar neman tallafin kuɗaɗe dala 100,000 ga wannan hukuma.”
Ya ce duk mai son bayar da gudummawa, ƙofa a buɗe ta ke. Amma ba zai taɓa bada kai bori ya hau ba.
PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai, Mohammed Garba, amma ba ta same shi ba.