GOBARA DAGA TEKU: Majalisar Legas ta yi fatali da sunayen kwamishinoni 17, bayan Musulman Legas sun yi ƙorafin danniya da wariya

Majalisar Dokokin Jihar Legas ta yi fatali da sunayen kwamishinoni 17 daga cikin 39 ɗin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya aika mata domin tantancewa.
Daga cikin waɗanda ta yi fatali da su ɗin, akwai guda shida waɗanda kwamishinonin Sanwo-Olu ne a zangon farko, yanzu kuma ya ke so su maimaita.
Kakakin Yaɗa Labaran Majalisar Dokokin Jihar Legas, Bisola Branco-Adekoya ce ta fitar da wannan sanarwa, kuma ta aiko wa PREMIUM TIMES.
Fiye da kashi 50 cikin 100 na waɗanda aka yi fatali da su, sun yi aiki tare da Sanwo-Olu a zangon sa na farko. Yayin da shida tsoffin kwamishinonin sa ne, wasu kuma mashawartan sa ne na musamman a zangon farkon.
Daga cikin sunayen 39 da Gwamna Sanwo-Olu ya aika, Majalisa ta tantance 22 kaɗai, ta yi fatali da 17.
“Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Midashiru Obasa, ya ce tantancewar da yin fatali da wasu ya biyo bayan ƙa’idojin da Kwamitin Tantancewa na Majalisa ya yi aiki da su, a ƙarƙashin Bulaliyar Majalisa, Fatai Mojeed”.
Sai dai kuma sanarwar ba ta ce an ƙi tantance su ne saboda ƙoƙarin da Musulman Legas suka yi cewa Gwamna Sanwo-Olu ya naɗa kwamishinoni 39, amma 31 Kiristoci, 8 Musulmai.
Zargin Nuna Bambancin Addini Da Musulman Legas Ke Wa Gwamna Sanwo-Olu:
Farkon watan Agusta ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Ƙungiyar Malamai ta Jihar Legas sun ƙi yarda a naɗa Kwamishinoni 31 Kiristoci, 8 Musulmai:
Rikici ya na ƙara kunno kai tsakanin Kungiyar Malaman Addinin Musulunci ta Jihar Legas da kuma Gwamnatin Babajide Sanwo-Olu.
Duk da dai dama tun bayan hawan sa zango na farko su ke ƙorafi kan zargin fifita Kiristoci fiye da Musulmai a gwamnatin sa, sai ga shi kuma lamarin ya ƙara ƙarfi sosai tun bayan da Gwamna Sanwo-Olu ya fitar da sunayen Kwamishinonin Jihar Legas, ya aika wa Majalisar Dokokin Legas domin tantancewa.
Sai dai kuma tuni a wani taro da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Malaman Legas mai suna JMT ta yi, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ansar-Ud-Deen na Ƙasa, Abdrahman Ahmad, sun yi fatali da sunayen kwamishinonin da Sanwo-Olu ya aika da su, tare da cewa gwamnan ya ƙara fitowa da nuna bambanci da ƙiyayya a fili ga Musulman Jihar Legas, waɗanda mafi yawan su ne ma su ka zaɓi APC, ba Kiristoci ne su ka zaɓe ta ba.
Ahmad Yahaya a ce ba tun yau Sanwo-Olu ke fifita Kiristoci a kan Musulmai wajen naɗe-naɗe ba, amma dai sunayen kwamishinonin da ya fitar a yanzu ya nuna lamarin gwamnan har ma akwai rainin wayo a ciki.
A cikin sunaye 39 da Gwamna Sanwo-Olu ya aika da su Majalisa, 8 kaɗai ne Musulmai, saura 31 Kiristoci.
Dama kuma kafin ƙungiyar ta malaman jihar Legas ta nuna fushin ta, sai da majalisar dokokin Legas ta maida sunayen, tare da yin ƙoƙarin cewa babu adalci a zaɓen kwamishinonin, domin an manta da wasu ƙananan hukumomin da gangan.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron ƙungiyoyin addinin Musulunci na Legas, akwai Babban Mufti na CIO, Dhikrullah Shafi’i, Isiak Tejidini daga Rahmatu Islamiyyah, sai AbdulJaleel Olori-Aje na Ƙungiyar Ƙwararru Musulmai, sai Farfesa Isiaq Akintola wanda ya wakilci MURIC.
Sauran sun haɗa da Muhammad Basheer daga Zumratul Muhmineen, Isma’il Yusuf daga Ƙungiyar Musulmi ta Yankin Mainland, AbdulGafaar Muslideen daga Da’awah, Amina Muhammad daga Al-Furqan, da sauran wasu da dama.
“Kashi 60 bisa 100 na al’ummar Jihar Legas Musulmi ne. Kuma su ne suka tsaya tsayin daka su ka ha cewa an samu nasara a zaɓen da ya gabata. Domin Kiristoci ba su zaɓi wannan gwamnatin ba, saboda haushin Muslim-Muslim da aka yi a Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa.” Cewar Ahmad.
“Mu na sanar da cewa gaba ɗaya ɗaukacin Musulmai na Jihar Legas mun yi fatali tare da rashin yarda da sunayen kwamishinonin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya aika da su Majalisa.
“Mu na kira da janye sunayen, a sake duba lamarin, domin ba mu yarda duk da mu ne kashi 60 bisa 100 na jihar Legas ba, amma a ce wai za a naɗa Musulmai 8 Kwamishinoni, Kiristoci kuma waɗanda ba su zaɓi wannan gwamnatin sosai ba, a ce za a naɗa Kwamishinoni 31 a cikin su.”
Ya ce dama Gwamna Sanwo-Olu ya daɗe ya na nuna masu bambanci da addinanci, kuma sun sha yi masa ƙorafi, amma ba ya yi masu adalci.
A wannan karo, Ahmad ya ƙara da cewa ɗaukacin Musulman Jihar Legas ba su yarda da abin da gwamnan ke ƙoƙarin yi masu na rashin adalci da nuna fifita wani addini a gwamnatin sa ba.
“Babu wanda ya ba Musulmai ko sisi a lokacin zaɓe. Haka mu ka riƙa bi muna cewa a zaɓi APC da Gwamna Sanwo-Olu.”
Sai dai kuma a tattaunawar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Legas ya yi da PREMIUM TIMES, Akosile ya jaddada cewa ba da gangan Sanwo-Olu ya ware wani addini ba. Ya ce ya bi tsarin cancanta ne da kuma raba-daidai da ɓangaren mata da na matasa.
Ya ce amma tunda ƙorafe-ƙorafe sun kunno kai, za a duba. “Domin a yanzu haka ana tuntuɓar shugabannin addinin Musulunci ɗin domin a yaye masu damuwar su. Kuma na tabbata daga ƙarshe abin da zai biyo baya, za a daidaita, babu wani ɓangaren da zai yi wani ƙorafi.” Inji shi.