GARKUWA DA ƊALIBAI: Mahukuntan Kwalejin Nuhu Bamalli sun sanar da rufe Kwalejin daga ranar Juma’a

Darektan Hulda da Jama’a na Kwalejin Nuhu Bamalli a madadin shugaban Kwalejin, ya sanar da rufe makarantar daga ranar Juma’a, 11 ga Yuni.

Wannan sanarwa ya biyo bayan harin sa da ƴan bindiga suka kai makarantar ne ranar Alhamis da dare.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahara suka afka makarantar dake UPE suka arce da ɗalibai da wasu malamai ranar Alhamis da dare.

Wani da ga cikin daliban da aka harba da bindiga mai suna Ahmad ya rasu awowi bayan an kwantar dashi a asibiti.

Sanarwar ta ce dakatarwar bai shafi dalibai dake shirin rubuta jarabawar IJMB da jami’ar ABU ke shiryawa ba wanda zasu fara a makon gobe.

A karshe an umarci dalibai su tattara su koma gida sai gwamnati ta sake buɗe makarantar kuma.

Rahotanni da sanyin safiyar Juma’a sun nuna cewa wasu ƴan bindiga sun dira Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin jihar Kaduna inda suka arce da wasu malamai biyu sannan suka kashe wani ɗalibi.

Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar Malamai Kwalejin Engineer Kofa, a wata ƴar gajeruwar takarda da ya raba wa manema labarai a Kwalejin ya ce maharan sun arce da malamai biyu sannan sun harbi wasu dalibai biyu.

Wata malama a jami’ar, Hadiza Mohammed ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa har yanzu ba a samu ainihin adadin yawan waɗanda suka bace tukunna domin ana ci gaba da bincike.

Sai dai sanarwar da ak fitar an ce wata mata da ƴaƴan ta biyu sun bayyana da safiyar Juma’a, bayan an sace su cikin dare.

Ta ce ko da yake ba ta zaune a cikin harabar Kwalejin dake UPE, tun a daren jiya ake gaya mata a waya cewa mahara sun dira makarantar kuma suna harbe harbe.

Ta kara da cewa ana nan ana ci gaba da yin bincike domin sanin yawan wadanda suka bace ba a gansu ba haryanzu.