GARGAƊI GA ƳAN NAJERIYA: Korona ba ta tafi ba, har yanzu dokokinta na nan daram a kasa – Gwamnati

Kwamitin dakile yaduwar cutar Korona ta kasa PSC ta bayyana cewa Korona bata tafi ba kuma dokokin da gwamnati ta saka domin dakile yaduwar cutar yana nan daram a kasar nan.

Shugaban kuka da aiyuka na kwamitin Mukhtar Muhammed ya sanar da haka a hira tashar ‘Channels’ ranar Talata.

Muhammed ya karyata labaran da wasu gidajen jaridu ke yadawa cewa wai ‘yan Najeriya ne kadai ke kiyaye dokokin dakile yaduwar Korona.

Ya ce wasu kasashe masu ci gaba sun dakatar da dokar saboda yawan mutanen da suka yi allurar rigakafin cutar a kasashen su amma zuwa yanzu akwai kasashe 85 dake kiyaye dokar dakile yaduwar cutar a kasashen su.

“Sannan akwai kasashe 30 da har yanzu suke sa matafiya killace kansu kafin su fara yawo a gari kamar su Canada, China sannan da wasu kasashe a Afrika kamar su Ghana da Najeriya.

Yaduwar cutar a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa zuwa yanzu mutum 266,283 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,155 a jihohin 36 da Abuja.

Hukumar ta kuma ce zuwa ranar 19 ga Nuwamba gwamnati ta yi wa mutum 55,278,769 allurar rigakafin Korona inda a ciki mutum 12,522,593 daga ciki basu kammala yin rigakafin ba a kasar nan.

Muhammed ya ce har yanzu kwamitin PSC tare da hadin gwiwar hukumomin da ma’aikatu ta ci gaba da daukan matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Ya ce har yanzu mutane na kamuwa da cutar kuma cutar ta ci gaba da kisan mutane sai dai yawan mutanen dake kamuwa da cutar da yawan da suke mutuwa a dalilin kamuwa da cutar ya ragu a Najeriya da duniya gaba daya.