Ganduje ya yi min rana, ba zan yi masa dare ba, dalilin da ya sa na yakice kaina daga su Shekarau kenan – Kabiru Gaya

Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Kabiru ya bayyana cewa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yi mai abinda ba zai iya yi masa butulci ba yanzu koma menene ya faru a tsakani.

Gaya ya ce ” Ganduje yayi rana a zaben 2019, dalilin sa na koma majalisa, ba zan iya yi masa butulci ba.

” Mun fara kungiyar tare da su Shekarau amma daga baya na zame kaina daga cikin su, na fice daga wannan tafiya, saboda na ga shirme ne rubuta irin wannan wasiƙa da muka yi wa gwamnan jiha sukutum.

” Kira na garesu shine su zo su tsuguna da guiwowin su bibiyu su tuba so roki Ganduje, a sake yi musu wankan tsarki a dawo aci gaba da tafiyar tare.

Ka bamu dama mu yi maka wannan fadar – Ado Doguwa

Shugaban masu rinjaye a majalisar tarayya, wanda ɗan asalin jigar Kano ne, Ado Doguwa, ya roki gwamnan jihar ya bashi dama tare da na kusa da shi su gurza wa yan adawar sa rashin mutunci.

Ado Doguwa ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke maida wa wata kungiya karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau da ke korafin APCn Kano ba ta yi da su.

” Ni fa a nawa ganin hakurinka ne ya yi yawan gaske maigirma Gwamna Ganduje, amma in ba haka ba, ni ka bamu dama mu yi maka wannan fadar kawai”

Martanin Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yi wa tsohon gwamna sanata Ibrahim Shekarau da ƴan kungiyarsa dake adawa da shugabancin sa a Kano kakkausar martani mai raɗaɗin gaske.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa gwamna Ganduje ya zargi sanatoci da ƴan majalisun da ke adawa da shi da yadda ake gudanar da APC a jihar da fakewa da gazawarsu suna cewa wai ba ayi da su a jam’iyyar.

” Ku dai ku faɗi gaskiya, ba nine matsalarku ba, gazawarku shi ke bibiyarku. Kun yi watsi da talakawan da suka zabe ku. An baku kuɗaɗen talakawa kuzo ku yi musu aiki kun lunkume su, yanzu kuna fakewa da ai nine kaza, Ganduje ya yi kaza.

” Babu ruwa na, da kun fito wa talakawa da kuɗaɗen su da aka baku daga Abuja kun yi musu aiki da su da basu ki ku ba. Da ma baku da farin jini ne a shiyyoyin ku.

Korafin Sanata Shekarau

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta faɗa cikin tsaka mai wuya, bayan wasu jiga-jigan jam’iyyar, Sanata Ibrahim Shekarau, Sanata Barau Jibrin da wasu ƴan majalisar dake wakiltar jihar Kano a majalisar Tarayyar sun zargi gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da yin gaban kansa ga al’amuran jam’iyyar ba tare da tuntuɓar su ba.

Ƴan majalisan sun wanda suka yi taron gaggawa a Abuja sun aikawa shugaban jam’iyyar na kasa, Mala Buni wasikar sanin matsayin su game da halin da jam’iyyar ke ciki a jihar Kano.

A cikin wasikar, sun koka kan yadda gwamnan jihar tare da makarraban sa a jigar suke yin gaban kan su ba tare da yin shawara da kowa ba.

” Kowa ya san irin gudunmawar da muka bada a zaɓen 2019. Amma bayan an gama zaɓen shi kenan aka wancakalar da mu. Ganduje ya kama gaban sa, sai yadda ya so ya ke yi da APC a Kano. Ba ya neman mu ballantana wai har yayi shawara da mu kan da wani abu da ya shafi jam’iyyar.

” Jam’iyyar Karkashin Ganduje ta ki cika alkawuran da ta ɗauka bayan nasara a zaɓe da aka yi a 2019. Wasu tsiraru ne ke tafiyar da harkokin jam’iyyar, kuma suna yin yadda suka ga dama ne abinsu ba tare da tuntuɓar ƴaƴan jam’iyyar ba.

” Saboda haka ba za mu amince da kokarin gudanar da zaben jam’iyyar na jihar Kano da ake shirin yi a karshen mako ba. Ba mu tare da waɗanda suka shirya zaben da kuma gwamnati akan haka.

Sai dai kuma shugaban Jam’iyyar Abddullahi Abbas ya ce kuturu yayi kaɗan, domin jam’oyyar ta kammala shiri tsaf don gudanar da zaben Kano.

” Ba kuma za mu matsar da zaben ba.” In ji Abbas