Ganduje Ya Naɗa Jarumin Kannywood Muƙamin Mai Bashi Shawara

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Mai girma gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa Alhaji Ishaq Sidi Ishaq a matsayin babban mai bashi shawara kan harkokin masana’antun ƙirƙira a jihar Kano.

Ishaq Sidi Ishaq dai Editan sashen Turanci na Zuma Times ne kuma babban jarumi a masana’antar Kannywood kuma mai bada umarni.
Ya yi karatu har zuwa matakin digirin farko a nan Najeriya daga bisani ya ƙetara zuwa ƙasashen Sin (China), Amurka, India da dai sauransu domin ƙarin karatu a bangaren harkokin fina-finai da masana’antun ƙirkira.
Ya kuma yi aiki da manyan gidajen Talabijin na ciki da wajen ƙasar nan kamar irin su Arewa 24, BBC Media Action, Farin Wata TV da dai sauransu. Sannan ya kasance cikin manyan masu rubuta labarin fina-finan Kudanci wato (Nollywood).

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaBuhari ya baiwa Babagana Kingibe sabon muƙami, ya cire shugaban hukumar NEMA