GA ƘOSHI GA KWANAN YUNWA: ‘Ba a taɓa noma masara mai yawa a Najeriya kamar cikin 2021 ba’ -Hukumar Abincin Amurka

Hukumar Bunƙasa Abinci ta Amurka, wato United State Department of Agriculture, (USDA), ta bayyana cewa tun da Najeriya ta samu ‘yanci cikin 1960, ba a taɓa noma masara mai ɗimbin yawa kamar cikin 2021 ba.

Masarar da aka noma a shekarar 2021 ta ɗara ta 2020 da kashi 16 bisa 100, kamar yadda rahoton USDA ya tabbatar.

USDA ta ce an samu bunƙasar noman masarar sakamakon haramta shigo da masara da Gwamnatin Tarayya ta yi, da nufin a bunƙasa samar da wadataccen abinci cikin gida, ta yadda za a rage ko a daina dogaro da shigo da abinci daga waje.

Wannan tsari kuwa Babban Bankin Najeriya CBN ne ya shigo da shi.ta yadda ta hana masu shigo da masara canjin dalolin shigo da masara. Ko da yake dai ba a hana su neman canjin dala a kasuwar ‘yan canji kuɗaɗe ba.

Wannan adadin yawan masarar da ake nomawa ya zo ne a daidai lokacin da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ta bayyana cewa za a yi wahalar abinci sakamakon ɓarkewar yaƙin Rasha da Ukraniya.

A ranar Talata ce Shugaban Kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya ce Najeriya ta yi shirin fuskantar ƙarancin abinci tsawon watanni uku, sakamakon mamayar da Rasha ta kai wa Ukraniya.

A baya-bayan nan Gwamnatin Tarayya ta ɗage takunkumin haramta fitar da masara zuwa ƙasashen waje.

Dangote ya ƙara da cewa a nan gaba tilas sai farashin takin zamani, alkama, masara da wasu kayan abinci ya tashi sama sosai.

“Yanzu haka Rasha ne samar wa duniya sinadarin ‘urea’ na haɗa takin zamani har kashi 30 bisa 100 da kashi 26 bisa 100 na sinadaran kanwa da sauran su.” Inji Dangote.

Ga Ƙoshi Ga Kwanan Yunwa:

A daidai lokacin da USDA ta fito da rahoton cewa an noma masara har metrik tan miliyan 11.6 cikin 2021, to kuma masarar ba ta taɓa yin tsada a Najeriya ba, tun bayan samun ‘yanci a 1960 sai a 2021 zuwa yanzu.

Idan aka kwatanta da masarar metrik tan miliyan 10 da aka noma a 2020, za a ga cewa ta 2021 ta haura kashi 16 bisa 100 kenan.

Masara dai ita ce kusan abincin da aka fi ci a Najeriya, kuma ana sarrafa ta ne ana yin abincin dabbobi da na kaji.

Cikin 2019 Afrika ta Kudu ce kaɗai ta fi Najeriya yawan noma masara, kuma a shekarar Najeriya ce ta 14 a duniya, amma kuma yawan wadda aka noma a shekarar ba ta wadaci Najeriya ba, har sai da aka samu giɓin ƙarancin mitrik tan miliyan 4 na masara a shekarar.

USDA ta ce masarar da aka shigo da ita a 2020 ta nunka wadda aka shigo da ita cikin 2019. A 2020 an shigo da metrik tan miliyan 1, a 2019 kuwa metrik tan 500,000 aka shigo da shi.

Sai da ta kai CBN ta daina bayar da canjin dala ga masu shigo da masara cikin 2020, saboda ganin yawan wadda aka shigo da ita.

Shugaban Ƙungiyar Masu Noman Masara da Sarrafa ta a Najeriya ( MAGPAMAN), Uche Edwin, ya ba su yi mamakin ganin yadda yawan masarar da ake nomawa a Najeriya ya ƙaru ba.

Ya ce ya kamata a yi la’akari da cewa a 2020 korona ta kawo wa noma cikas, a 2021 kuma CBN ya ƙara bayar da maƙudan kuɗaɗe ramce ga manoma a ƙarƙashin shirin ‘Anchor Borrowers’.