FESHIN MUTUWA: Manoman Najeriya na amfanin da maganin ƙwarin da aka haramta fesawa a ƙasashen Turai – Rahoto

Wani sabon rahoto ya tabbatar da cewa kusan kashi 40 bisa 100 na magungunan kashe ƙwarin da manoman Najeriya ke fesawa, duk an haramta fesa su a ƙasashen Turai.

Rahoton Sa-ido Kan Amfani Da Maganin Kashe Ƙwari A Najeriya (Alliance for Action on Pesticide in Nigeria), wanda aka ƙaddamar a ranar Alhamis ne ya jaddada haka.

An bayyana haka a taron wanda AAPN da Trade Network Initiative su ka shirya, tare da goyon bayan Heinrich Böll Stiftung da aka fi sani da HBS, a Abuja.

“Ƙashi 40 na magungunan kashe ƙwarin da ake sayarwa kuma ake feshin su a Najeriya, duk an janye su daga kasuwannin Turai, saboda an haramta amfani da su a can ƙasashen.” Haka rahoton ya bayyana.

Rahoton dai na ƙunshe da binciken da aka yi a Kano, Oyo, Ebonyi da Benuwai. Kuma ya nuna kashi 40 na magungunan kashe ƙwarin, har samfuran magani 57 cikin 402 da aka haramta amfani da su, duk ana amfani da su a Najeriya.

Da yawa daga cikin su duk dangogin magunguna ne masu guba, cutarwa da gurɓata abinci da lafiyar jama’a (HHPs).

Waɗannan nau’ukan magungunan ƙwari babbar illa ce ga lafiyar mutane, dabbobi da yanayi.

Rahoton ya nuna samfuran magunguna 224 su na da illa sosai a jikin mutane, wasu kuma a jikin dabbobi da yanayi.

Sannan kuma rahoton ya bayyana cewa a fili irin waɗannan illoli da magungunan su ka yi a jikin mutane da yanayi su ke.

“Illar magungunan kashe ƙwari ta yi ajalin mutuwar rayuka 270 a Jihar Benuwai, sakamakon gurɓata kogi da gubar maganin kashe ƙwarin da ƙasashen Turai su ka hana amfani da shi.”

Rahoton na AAPN ya ce samfurin maganin kashe ƙwarin da aka fi amfani da shi mai matuƙar illa, shi ne chlorpyrifos, fungicide mancozeb da herbicide glyphosate, Waɗanda dukkan su an bayyana cewa su na da matuƙar hatsari sosai.

Matsalolin Da Ke Kawo Cikas Wajen Yi Wa Magungunan Kashe Ƙwari Dabaibayi A Najeriya:

A wurin taron, an tattauna matsalolin da ke kawo cikas wajen sa dokokin kula da magungunan kashe ƙwari da kuma amfani da ƙa’idojin da dokokin su ka shimfiɗa.

Ahmed Munir, Ɗan Majalisar Tarayya, wanda ya wakilci Muntari Ɗandutse, Shugaban Kwamitin Majalisar Tarayya Kan Harkokin Noma, ya yi magana na ya ce akwai buƙatar akwai buƙata ɓangarorin hukumomin gwamnati da cibiyoyi su riƙa aiki tare domin ƙarfafa Dokar Magungunan Kashe Ƙwari a Najeriya.

Mutane da yawa daga hukumomin gwamnati da ma’aikatu da ƙungiyoyi sun yi jawabai da ƙarin haske a wurin taron.