Farfesa Gwarzo ya zama Wazirin Hausawan Turai

Farfesa Adamu Gwarzo ba ba ɓoyayyen suna bane a musamman nahiyar Afrika idan ana maganan ɗaukaka ilimi da inganta rayuwar musamman matasa ba a Najeriya ba har da kasashen Afrika ba ki ɗaya.

A Asabar 4 ga Disambar 2021 mai martaba sarkin Hausawan Turai Alhaji Sirajo jan kado ya daga Darajar sarautar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo daga Sardaunan sarkin Hausawane Turai zuwa Wazirin sarkin Hausawan Turai.

Bukin nadin sarautar sabon wazirin wanda aka Gudanar dashi a fadan sarkin Hausawan Turai dake birin Paris babban birnin kasar France, ya samu halartar Dimbin masoyan sabon wazirin sarkin Hausawan na Turai wanda shine dama tsohon Sardaunan kuma tsohon sardaunan Turai yayi Armashi kwarai da Gaske

Ali Kakaki wanda ya ruwaito wannan kasaitaccen bukin naɗi na wannan jarumi ya ce a madadin sarkin hausawa ga maharta taron Santurakin Turai Alhaji Aminu Fanda ya bayyana cewa masarautar na turai ta yanke shawaran daga Darajan sarautar farfesa Gwarzo ne sabo da yadda yake Dawainiyya da masarautar da yayanta baki daya da sauran Al-Ummah a fadin Duniya baki daya,

Santukin ya kara da bayyana ma mahalarta taron bukin nadin sarautar cewa A matsayin Farfesa Adamu Gwarzo na Shahararen Dan jarida wanda har ya taba rike shugaban kungiyar kare hakkin yan jarida na Afrika sau biyu, yanzu haka kuma shine mamallakin Rukunin jami’oin Maryam Abacha American University dake Niger da Nageriya sannan kuma da jamiar Franco-British University. Kaduna Nigeria haka kuma shine shugaban kungiyar jami’oin Afrika masu zaman kansu ,

Wazirin sarkin Hausawan Turai farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya Godewa Allah (SAW) da ya bashi rai da lafiya da kuma ikon taimakon Al-ummah ba tare da wani Gajiyawa ba, sannan ya godewa sarkin Hausawan Turai da yan majalisar masarautar Turai da suka Daga Darajar sarautarsa daga sardauna zuwa Waxiri

Shugaban rukunin jami’oin ta Maryam Abacha American university dake Niger da Najeriya ya kuma Godewa wadanda suka halarcin taron bukin daga Darajar sarautarsa zuwa waziri, ” haka kuma ina kara mika Godiya ta musamman ga Dimbin masoya da suka rika kiranmu ta wayar GSM suna tayani murna da farin ciki da kuma wadanda suka rika aiko mun da sakon Taya murnarsu ta hanyonyin kafafen sada zumunta , Nagode ! Nagode !! Nagode Allah ya Saka muku da Alhrensa sannan ya kara dankon zumuncin dake tsakanin a daku ya ku jamaa.