Farfesa Gwarzo ya jinjina wa shugaba Tinubu bisa naɗin Farfesa Tahir Mamman, ministan Ilimi

Shugaban rukunin jami’o’in Maryam Abacha dake Kano da Nijar, da kuma jami’o’in Canadian Abuja, da British-Franco dake Kaduna, Farfesa Adamu Gwarzo, ya jinjina wa shugaban kasa Bola Tinubu, bisa naɗa Farfesa Tahir Mamman, ministan Ilimi da ya yi.
A sanarwar taya murnar, Farfesa Gwarzo, ya ce ” Ina da yakini cewa shugaba Tinubu ya yi zaɓen nagari ba Farfesa Tahir Mamman ministan Ilimi da ya yi. Wannan mukami da aka ba shi ya cancanta, domin kwararre ne a harkar ilimi sannan babban lauya ne.
” Ina mai matuƙar ta ya Farfesa Tahir Mamman murnar samun wannan mukami tare da fatan Allah ya ta ya shi riko. Amin.