Facebook ya cire labaran karya sama da miliyan 18 kan Korona – DUBAWA

Manajan tantance labaran karya na kamfanin Facebook na reshen Yankin Gabas Ta Tsakiya, Afirka da da kasar Turkiyya, Tom Nvumba-O’Bryan, ya bayyana cewa sun cire shafuka da labarai sama da miliyan 18 wadanda ke yada labaran karya kan cutar Korona daga dandalin Facebook.

Mr. Nvumba-O’Bryan ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi kan hanyoyin amfani da fasaha wajen yaki da yada labaran karya a wani taro da aka yi a Abuja.

DUBAWA ce ta shirya taron na wuni biyu, wanda ke da burin hada kan ‘Yan jarida, malaman makarantu, masu bincike da ma jama’a baki daya wajen tattauna matsalolin da ke tattare da yada labaran karya da ma irin yinkurin da ake yi na dakile irin haka.

Mr Nvumba-O’Bryan ya ce kamfanin Facebook wanda yanzu ake kira Meta Platforms, Inc, yana amfani da matakai uku wajen tantance labaran karya kamar haka: Ragewa, cirewa da sanarwa.

Ya ce: “Daya daga cikin dalilan da ya sa muke abota da kungiyoyin da ke tabbatar da sahihanci labarai shi ne irin taimakon da mu ke samu wajen tantance labaran karya da yin watsi wadanda ba su da tushe.”

Jami’in ya ce ko da yaushe suna cire shafukan da ke wallafa labaran karya. Shafukan da ke karkashin kamfanin Meta Inc., wadanda ke hada-hada da sunan Meta wanda kuma aka fi sani da Facebook babban kamfanin fasaha ne mai rassa daban-daban da ke da mazaunin shi a Menlo Park jihar Carlifornia. Kamfanin ya mallaki shafukan Facebook, Instagram, WhatsApp da ma wasu sauran kananan kamfanoni.

A na sa jawabin, Tobi Oluwatola, babban darektan riko na Cibiyar bincike a aikin jarida na Premium Times ya mika godiyarta ga wadanda suka ba da tallafin kudin shirya taron da mahalarta, wadanda ya ce dukansu na da buri daya, wato yaki da bazuwan labaran karya a yankin yammacin Afirka.

Yayin da ya ke jaddada cewa “aikin da ‘yan jarida ke yi na da mahimmnaci a al’ummar yau,” ya kara da cewa labarai marasa gaskiya hadari ne ga kowace irin al’umma wanda ke bukatan sa ido na musamman.

Jochen Luckscheiter, babban darektan giduauniyar Heinrich Böll a Najeriya ya nuna farincikin shi da taron abin da ya ce ya zo daidai da manufofin gidauniyar kuma za ta cigaba da tallafawa ayyukanta.

Ya kuma jadddada bukatar fahimtar yanayi da kuma suffan da irin wadannan labaran ke dauka a kowace al’umma.

“Ya na da mahimmanci a gano dalilai da halayen da ke baiwa labaran karya ikon yin irin tasirin da su ke yi kuma wadannan ne za su kasance batutuwan da ya kamata a yi amfani da su a duniya baki daya,” in ji Mr Luckscheiter.