EFCC ta sake damƙe Femi Fani-Kayode a harabar kotu

Hukumar EFCC ta sake kama tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, bisa zargin sa da ake yi da laifin fojare ɗin buga takardun bogin da ya gabatar wa kotu, inda ya yi ƙaryar rashin lafiya, don ya kauce wa tuhumar zambar naira biliyan 4.9.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito a ranar Talata cewa an sake kama Femi Fani-Kayode a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, jim kaɗan bayan an ɗage shari’ar sa da ake yi zuwa ranar 24 Ga Fabrairu.

Rahotanni sun ce an zarce da Fani-Kayode kai-tsaye zuwa Ofishin EFCC da ke Legas.

Ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren bai yiwu ba, saboda an kasa samun lambobin sa kafin a buga wannan labari.

Kakakin Yaɗa Labaran Fani-Kayode, mai suna Florida Nzenwa cewa ba za ta iya cewa komai a kan lamarin ba tukunna, har sai ranar Laraba.

Ana tuhumar Fani-Kayode da bugawa da kuma mallakar takardun bayanan likita na jabu, domin ya kauce wa zuwa kotu amsa tuhumar da ake yi masa.

Tuhumar Da Ake Wa Fani-Kayode: Ana tuhumar sa da laifin zambar naira biliyan 4.9 tare da waɗansu mutum biyu, da su ka haɗa da tsohuwar Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Nenadi Usman, tsohon Shugaban Kungiyar Ciyamomin Ƙananan Hukumomin Najeriya (ALGON), Yusuf Ɗanjuma.

Ƙin halartar kotu da Fani-Kayode ya yi ya sa kotu ta ci tarar sa naira 200,000.

Zaman baya bayan nan da aka yi ne lauyan Fani-Kayode ya shaida wa kotu cewa wanda ya ke karewar ba zai samu damar zuwa kotu ba, saboda ya na kwance a babban asibitin Kubwa, ba shi da lafiya. Kuma ya gabatar ta takardun likita tun kafin wannan zaman.