EFCC ta damƙe wasu Ƴan ruguguwa da katin ATM 1,144 a filin jirgin saman Kano

Jami’an Hukumar EFCC sun kama wasu mutane uku, waɗanda ta samu da katin ATM na bankuna daban-daban har guda 1,144, a filin jirgin saman Kano.

EFCC ta ce an kama waɗanda ake zargin a lokacin da su ke ƙoƙarin yin sumogal ɗin katin sama da duhu ɗaya wajen ƙasar nan.

Kakakin Yaɗa Labaran EFCC Wilson Uwujaren ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa an kama waɗannan ‘yan ruguguwa tun a ranar 24 Ga Nuwamba, da kuma 1 Ga Disamba.

Mutanen uku da aka kama a cewar EFCC, sun haɗa da Abdullahi Usman, Musa Abubakar da kuma Abdulwahab Auwalu.

Yayin da aka damƙe Abubakar lokacin da ya ke ƙoƙarin hawa jirgi zuwa Dubai ɗauke da katin ATM 714, shi kuwa Usman ya na kan hanyar sa ta neman tafiya Saudi Arabiya ne EFCC ta damƙe shi da katin ATM 298.

Shi kuma Auwalu an same shi ɗauke da katin ATM 132, lokacin da ya ke ƙoƙarin hawa jirgin Ethiopian Airlines zuwa birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya.

“Dukkan wadanda ake zargin dai nan ba da daɗewa ba za a gurfanar da su a kotu da zaran an kammala bincike.” Inji Uwujaren.

Ruguguwar Safarar Katin ATM Zuwa Ƙasashen Waje:

Idan ba a manta ba, cikin watan Satumba, 2020 EFCC ta kama wani ɗan harƙalla da katin ATM 2,886 a filin lokacin da ya ke ƙoƙarin fita da su zuwa Dubai.

Wanda aka kama ɗin mai suna Ishaq Abubakar, jami’an kwastan ne su ka damƙe shi a filin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas, su ka damƙa shi ga EFCC domin bincike da kuma gurfanarwa kotu.