EFCC da Bankin Sterling sun maida kuɗaɗen albashin da Gwamnan Kogi ya ɓoye bai biya ma’aikata ba

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar cewa Bankin Sterling ya maida masa zunzurutun naira biliyan 19.3, wadda EFCC ta bankaɗo cewa kuɗaɗen tallafin biyan ma’aikata albashi ne da Gwamnatin Tarayya ta ba Jihar Kogi, amma Gwamna Yahaya Bello ya ɓoye kuɗaɗen a Sterling Bank.

Cikin wata sanarwa da Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Juma’a, ya ce CBN ya tabbatar da karɓar kuɗaɗen daga Sterling Bank.

Tun da farko dai jihar Kogi ƙarƙashin Yahaya Bello ta kasance tsawon watanni ba ta biya albashi ba.

Sai gwamnatin tarayya ta bayar da kuɗaɗen rufin asirin da za a biya ma’aikatan jihar albashi.

Maimakon Gwamna ya sa a biya, sai ya sa aka ɓoye kuɗaɗen a wani asusun da a kullum za a riƙa samun kuɗin ruwa, maimakon a ajiye cikin asusun albashin ma’aikata.

Yayin da EFCC ta gano inda Yahaya Bello ya ɓoye kuɗaɗen, ta garzaya Babbar Kotun Tarayya a Legas, inda ta nemi a ba ta damar riƙe kuɗaɗen.

A ranar 31 Ga Agusta ne Mai Shari’a TJ Ringim ya kulle asusun, ya hana Gwamnatin Kogi amfani da kuɗin.

Daga baya EFCC ta nemi kotu ta buɗe asusun, tare da umartar Sterling Bank ya maida kuɗaɗen Asusun Gwamnantin Tarayya a CBN.

Cikin watan Oktoba ne Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya a Legas ya bayar da umurnin.

Yahaya Bello wanda ke haƙilon neman takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC, ya kasance a cikin wannan shekara ya na ta bindiga da kuɗaɗen jihar wajen yi masa kamfen, tun ma kafin lokacin kamfen ɗin ya gabato.

A yanzu haka ɗimbin ‘yan fim ɗin Kannywood sun karkata wajen shirya masa wakokin kamfen birjik, waɗanda ake kashe makudan miliyoyin kuɗaɗe wajen shirya su.