Duniya za ta afka cikin mummunar yanayi idan ba a kawo karshen yaduwar cututtukan da basu jin magani ba – Gargadin WHO

A taron dakile yaduwar cututtukan da basu jin magani na duniya da aka yi a Abuja ranar Litini Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga kasashen duniya da su yi gaggawar daukan matakai da za su taimaka wajen dakile yaduwar cututtukan da basu jin magani ba musamman wadanda maganin ‘Antibiotics’ ke warkarwa.

WHO ta yi wannan kira ne ganin yadda ake samun karuwar cututtukan da basu jin magani a duniya.

Wakilin WHO zuwa Najeriya Walter Mulombo ya ce rashin daukan mataki game da wannan matsala ka iya hana likitoci yi wa mutane fida, kula da masu fama da cutar daji da kula da jariran da ake haifa bakwaini.

Wayar da kan mutane kan Shan maganin Antibiotics yadda ya kamata.

Mulombo ya ce wayar da kan mutane na cikin hanyoyin da za su taimaka wajen hana yaduwar cututtukan da basa jin magani.

Bincike ya nuna cewa duk shekara cututtukan da basu jin magani na yin ajalin mutum 700,000 inda a ciki akwai mutum 230,000 dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar tarin fuka da baya jin magani.

Wani babban likitan dabobbi a ma’aikatar noma mallakin gwamnatin tarayya Peter Umanah ya yi kira ga gwamnati da ta ware kudade domin yakan cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin rashin shan maganin Antibiotics yadda ya kamata.