Duk wani mai takarar kujerar siyasa da na naɗa a gwamnati na ya ajiye aiki daga yau zuwa 16 ga Mayu -Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci duk wani minista ko jami’in gwamnati da ke neman takarar shugaban Kasa, gwamna ko majalisar jiha da na kasa, ya ajiye aiki nan da ranar 16 ga Mayu.
Ministan yaɗa labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana haka wa manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa a Abuja.
” Kamar yadda aka yanke a zaman majalisar zartaswa, Buhari ya umarci duk wani wanda shine ya naɗa kuma ya fito takarar wata kujera a kasarnan, sai ya ajiye aikin sa nan da ranar Litinin mai zuwa wato 16 ga Mayu.
Cikin wadanda za su ajiye muƙamansu akwai ministan Shari’a Abubakar Malami wanda yake takarar gwamnan jihar Kebbi.
Akwai minista Kwadago, Chris Ngige, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Minista Kimiya Ogbonnaya Onu, da dai sauransu.