Duk wanda yayi mana Kazafi ko Sharri, Raka’a biyu na ke yi ranar Alhamis da dare in hada shi da Allah – Inji El-Rufai

Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce gwamnatin sa ba za ta tsangwami ko kuma ta bi wadanda suke yi mata bita-da-kulli da sharri ba, iyakar ta hada koma waye da Allah.

” Duk wanda ya yi mana kazafi, yana yi mana karya a don wata muguwar manufa ta sa, ba za mu bishi da sharri ba ko kuma bita da kulli, iyakar mu tashi cikin dare ranar Alhamis mu yi raka’a biyu mu hada shi da Allah. ”

Bayan haka El-Rufai ya yi karin Haske kan wasu ma’aikatan da ake biyan su rabin albashi cewa an kama wasu ma’aikata sama da 9000 da ke da matsaloli a takardun su da ko asusun ajiyar su.

Gwamna El-Rufai ya ce da zaran an kammala tantancewa ma’aikata za a koma jin dadin da samun albashi a kan lokaci.

Da yake magana game da zanga-zangar kungiyar kwadago suka yi, El-Rufai yace kudi aka basu su zo su tada hankalin mutanen Kaduna.

” NLC sun zo Kaduna ne domin sun ci kudin wasu kuma dole sai sun yi yajin aikin. Gwamnatin Tarayya ta kasa hukunta NLC, amma kuma mu sai mun bi wa mutane hakkunan su saboda sun karya doka ce tun farko.

” Dalilan da NLC suka fadi karya ne. Idan NLC suka dawo Kaduna sai sun dandana kudar su.