Duk da ƙalubalen da mu ke fuskanta, Najeriya za ta ci gaba da zama ƙasa ɗaya dunƙulalliya – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin siyasa su riƙa sa kishin ƙasa da kare muradun Najeriya a zukatan su, da ya ke jawabi lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin rusasshiyar jam’iyyar CPC na jihohi, a fadar sa, Buhari ya ce “duk da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, za ta ci gaba da kasancewa ƙasa ɗaya dunƙulalliya.
Ya ce kishin ƙasa da yi wa ƙasa ɗa’a ne ginshiƙan kafa CPC, kuma su na nan ba su gushe ba.
“Ina yin kira ga ‘yan Najeriya kada su bari son ran da aka nuna tsakanin 1967 zuwa 1970, wanda ya haifar da asarar mutuwar fiye da mutum miliyan ɗaya ya maimaita kan sa.”
Ya ce ‘yan Najeriya sun kashe juna a wancan lokacin don dai a tabbatar cewa Najeriya ta ci gsba da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa ɗaya.
Ya ce bai yada ‘yan rusasshiyar jam”iyyar CPC bayan ta narke a cikin APC. Ya buga misalin cewa daga cikin ministocin sa na yanzu haka, akwai gyauron CPC iron Ministan Shari’a Abubakar Malami, Ministan Ilmli Adamu Adamu, Ministar Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Faruq da Ministan Harkokin Inganta Ruwa.
Shugaban ƙungiyar kuma tsohon shugaban rusasshiyar jam”iyyar CPC na Jihar Neja, ya jinjina wa Buhari.