DUBU TA CIKA: An cafke Kabiru da ke yin lalata da ƴara ƙanana ta dubura a Abuja

Hukumar Inganta al’umma dake babban birnin tarayya Abuja SDS ta cafke wani mutum da ya rika lalata da yara kanana har 19 ta dubura.
Mai rikon kwaryan shugabancin hukumar Sani Amar ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata a Abuja ya ce an kama mutumin ne a kauyen Karmajiji dake hanyar zuwa filin jiragen saman Abuja.
Ya ce an kama mutumin ne bisa ga umurin da karamar ministan Abuja Ramatu Aliyu ta bada.
Amar ya ce a ranar 19 ga Yuni ne aka kirashi daga kauyen Karmajiji cewa mazaunan kauyen sun kama wani mutum mai suna Kabiru dake lalata da yara kanana ta dubura.
” Mazauna kauyen sun ce Kabiru ya shahara wajen yin lalata da yara kanana maza masu shekaru 12 zuwa ƙasa da karfin tsiya.
“Sakamakon binciken da muka gudanar ya tabbatar mana da cewa Kabiru ya yi lalata da yara kanana maza har su 19 a wannan kauye.
Ya ce dubun Kabiru ya cika a ranar da ya lallabi wani yaro zuwa dakinsa da lemu da alawa, bayan sun shiga daki ya kulle kofa sannan ya nemi ya yi lalata da yaron da karfi da tsiya.
“Ihun da yaron ya rika yi ne ya sa mutane suka shigo dakin suka iske Kabiru na kokarin aikata wannan mummunar abu.
“A nan take bayan an kama shi yara da dama a kauyen ke fada cewa Kabiru ya yi lalata da su ta dubura.
“Wani yaron ya ce Kabiru ya zuba maganin barci a taliyar indomine ya bashi. Bayan ya yi barci ya danne sa.
“Yaron ya ce ko da ya tashi daga barcin bai gane jikinsa ba sannan Kabiru ya bashi naira 50 domin ya yi amfani da ban dakin kasuwa. Yaron ya ruga gida ya sanar da iyayensa abinda Kabiru ya yi.
Amar ya ce hukumar su tare da ‘yan sandan a Wuye sun kama Kabiru Kuma sun hada da yaron da ya nemi ya danne sun damka su ga fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka domin ci gaba da bincike.