Dokar hana cin kasuwanni da ƴan acaba ya yi tasiri wajen rage ta’addanci a Kaduna – Sarkin Birnin Gwari

Sarkin Birnin Gwari Zubairu Jibrin Mai Gwari II ya yaba wa gwamnatin Kaduna ƙarkashin gwamnan jihar Nasir El-Rufai, kan wasu muhimman dokoki da ya saka a jihar domin daƙile hare-haren ƴan bindiga.

Mai Gwari ya faɗi haka ne a jawabin da yayi wa manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan kammala taron tsaro da aka yi a garin Kaduna ranar Laraba

” Ina tabbatar muku da cewa matakanbda gwamnatin Kaduna ta dauka na hana kasuwannin mako-mako ya yi tasiri matuƙa. Sannan kuma da hana masu hawa babura wato ƴan acaba zirga-zirga. Haka kuma toshe layukan waya yayi tasiri.

” Yan zu fa idan ƴan bindiga suka sace mutum ba kuɗi suke nema ba, sai suce a kawo musu abinci su sake shi. Yunwa ma kawai ya ishe su.