Diezani bata mallaki rigar maman da ya fi tsada a Duniya ba – Binciken DUBAWA

Kasa da makonni biyu bayan Daily Trust da Dubawa shafi mai binciken bankado gaskiyar labari suka wallafa abinda suka gano game da ko akwai rigar maman lu’u-lu’un da ake zargi ita ce mafi tsada a cikiin kayan da tsohuwar ministan man fetur Diezani Alison-Madueke za ta sadaukar wa hukumar EFCC ta tabbatar da gaskiyar sakamakon wannan bincike.

Rahoton da wata jarida ta wallafa ya yi zargin cewa daga cikin kayan da tsohuwar ministar wadda ake zargi da yin sama da fadi da dala biliyan biyu da rabi, har da “gidaje a Banana Island da ke jihar Legas.” Ya kara da cewa akwai rigunan aure 125, kananan rigunan sawa 13, rigunan maza 11, damarar tumbi 41, rigunan mama na musamman 11, da sauransu.

To sai dai mutane a shafukan soshiyal midiya sun yi zargin cewa daga cikin kayan ma akwai rigan maman da aka sanyawa masa lu’u-lu’u kuma irin shi ne mafi tsada a duniya domin farashin shi ya kai dalan Amurka miliyan goma sha biyu da rabi.

Binciken da Daily Trust da Dubawa suka buga ranar 7 ga watan Oktoba, 2021, ya bayyana cewa zargin wai tsohuwar ministar man fetur na da rigar maman da ya fi tsada a duniya karya ne.

Binciken ya samu tabbacin haka ne bayan ya bi diddigin gano tushen tarihin rigar mama mafi tsada a duniya zuwa wata rigar mama mai suna “heavenly star bra” a turance, wanda aka kirkiro a shekarar 2001 a kamfanin Victoria Secrets wani kamfanin rigunan mata na Amurka wanda Heidi Klum, bajamushiya kuma shahararriya a fanin kawa ta sanya lokacin wani bukin kwalisa a shekarar 2001.

Binciken ya gano cewa masu zargin Alison Madueke da mallakar rigar maman sun yi amfani da hotunan daya daga cikin wadanda kamfanin Victoria Secret ya kirkiro ne. Da aka nemi ji ta bakin ministan Shari’a, Kakakin ministan Uamr Gwandu ya yi mana karin harke akai in da shima ya karyata maganan. A yayin da shi kuma shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ranar laraba ya fayyace batun a daya daga cikin shirin tashar TVC mai suna “Your View” inda ya ce: “Sau da yawa kuna zargin mu da gudanar da shari’a a kafofin yada labarai amma a tunani na ya kamata a rika kamanta adalci wa kowa da kowa. Babu wata rigar mama. Mutane ne a shafukan Soshiyal Midiya fadin haka, amma ba gaskiya bane.”

Ya kuma kara da cewa: “Zan iya gaya muku wannan kyauta tunda ni ne jagoran binciken kuma ban ga wani abu kamar haka ba. Idan da akwai, da na sani. Ya kamata a ce na sani tunda ni na jagoranci binciken. Shi ya sa na ce daya daga cikin manyan matsalolinmu it ace halayarmu. Ya kamata mu canja dan a samu gyara.”