Dalilin daya sa aka katse hanyoyin sadarwar wasu layukan kira a Kananan hukumomin Sokoto 14 – Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana wa Muryar Amurka cewa sai da suka samu amincewar ma’aikatar Sadarwa ta kasa kafin aka katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Tambuwal Ya ce an yi haka ne saboda a toshe hanyoyin sadarwar da ‘yan bindiga ke amfani da shi wajen gudanar da ayyukan su na ta’addanci.

Kananan hukumomin da aka katse wa layukan sadarwa sun hada da Dange Shuni, Tambuwal, Sabon Birni, Raba, Tureta, Goronyo da Tangaza.

Dama kuma an toshe layukan sadarwa a jihar Zamfara Kaf din ta saboda yan bindiga.

Ita ma jihar Katsina ta sanar da toshe layukar sadarwar a Kananan hukumomi 13 a cikin makon da ya gabata.

Gwamnan Zamfara Matawalle wanda a baya shine ya rika yin kamfen din lallai ayi sulhu da ‘yan bindiga ya dawo daga wannan rakiya inda ya ce ba ‘yan bindigan ba mutane ne masu Alkawari ba. Tuni ya sakja hannu a takardar a ragargaje su.

Wakiliyar Premium Times, da take Sokoto ta ce lallai babu layin da ke tafiya har a cikin garin Sokoto, wato babban birnin jihar.

” Yanzu haka ina cikin garin Sokoto, kuma ina tabbatar muku cewa MTN ba ta tafiya. Itama Airtel ba ta tafiya saida ta yanar gizo akan samu a yi kira da Airtel.

A bisa wannan bayani, dakile hanyoyin sadarwar ya shafi har da cikin garin Sokoto kenan zuwa yanzu.