Dalilin da ya sa na wancakalar da APC, jam’iyyar El-Rufai da Buhari – Samaila Suleiman

Ɗan majalisan da ke wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar Tarayya Samaila Suleiman, da aka fi sani da Farar Aniya ya fice daga jam’iyyar APC.

A wasikar sanar da ficewar sa daga APC Honarabul Samaila ya ce rikicin da ya cukuikuye jam’iyyar APC a Abuja da ya sa yanzu haka aka samu rarrabuwar kai ya sa dole ya hakura da jam’iyyar.

” Ka katun jam’iyyar ku nan na hakura da ita. Zan kara gaba. Wannan shawara da na ɗauka ya zama dole ganin yadda jam’iyyar ta cukuikuye cikin ruɗani da rarrabuwar kai sannan ga rashin sanin ainihin nda aka dosa a jam’iyyar.

Samaila ya ce daga yanzu ba shi ba APC.

Sai dai kuma ba a nan gizo ke saka ba domin wani jigo a jam’iyyar PDP ya shaida da wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa jam’iyyar PDP ce ɗan majalisar zai koma domin har ya fara kwankwasa mata kofa yana so ya tsunduma cikin ta.

Ga dukkan alamu dai jam’iyyar PDP ce ya ke so ya koma kuma a can ya ke so ya yi takarar dan majalisa.

Wasu daga cin ƴaƴan jam’iyyar PDP sun bayyana wa wakilin mu cewa abin da kamar wuya domin Honarabul Shegu ABG ya na takarar kujerar a inuwar jam’iyyar kuma shi daɗaɗɗrn ɗan jam’iyya ne.