Dalilin da ya sa na kashe mijina- Fatima Abubakar, matar da ta kashe mijinta da guba

Wata matar aure ‘yar shekara 25 mai suna Fatima Abubakar da aka kama a Borno bisa zargin kashe mijinta, Goni Abbah, ta bayyana cewa ta kashe shi ne saboda ta gaji da auren.

Fatima ta lura cewa bata taba son auren ba, kuma Goni shine mijinta na biyu.

Ta ce, “Na rabu da mijina na farko saboda na tsani aure. Duk lokacin da na tashi na tuna cewa na yi aure, abin ya abin yana bani haushi. A wani lokaci sai na koma wurin iyayena don neman kashe auren amma kullum sai su mayar da ni, suna neman na yi hakuri.

“A wani lokaci, bayan wata biyu da na haifi ɗa na, sai na gudu na bar gida na tare a wani gini kango na kusan sati biyu, a nan nake kwana. Daga baya na koma gidan mijina. Ba wai bai kyautata min ba, kuma ba rigima muke yi ba. Mu biyu ne a gidan, ni ce matarsa ​​ta biyu kuma na aure shi tun 2021. Amma ni dai ina kyamar duk mutumin da ya kusance ni.

“A gaskiya ban san abin da ke damuna ba. Ko a yanzu da nake magana da kai ba na jin cewa ni ne na kashe shi,” ta fadi cikin kuka.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar, ya ce wanda ake zargin a cikin jawabinta, ta amsa laifin da ake zarginta da shi, inda ta ce ta sayi gubar ne a kasuwar Monday Market a lokacin da ta riga ta yanke shawarar kashe shi.

Ya ce an rubuta karar a matsayin laifin kisan kai a ofishin daraktan kararrakin jama’a kafin a gurfanar da ita a kotu.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan ta kama wanda ake zargin ne a ranar 19 ga watan Oktoba a Anguwan Doki.

Umar, ya ce wanda abin ya shafa, wanda shi ne Babban Limamin yankin, ya dawo daga masallaci ne a lokacin da wanda ake zargin, wadda ita ce matarsa ta biyu, ta hada guba a cikin abincinsa.

Ya bayyana cewa bayan Goni ya fara cin abincin ne lafiyarsa ta tabarbare.

Ya ce, nan take aka garzaya da shi asibitin kwararru na jihar inda aka ba shi kulawar gaggawa, amma abin takaici daga baya ya rasu bayan sun dawo gida.