Dalilin da ya sa muke zawarcin Shekarau ya dawo PDP, muka kuma ziyarci Tambuwal – Aminan Kwankwaso

Wasu daga ciki manyan aminan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Kwankwaso ƙarƙashin jagorancin Yunusa Dangwani da Yusuf Dambatta da Abubakar Danburan da kuma Hadiza Adado sun kaiwa Malam Ibrahim Shekarau ziyara a gidansa dake Abuja a Ranar Alhamis.

Sule Ya’u, Kakakin tsohon gwamna Shekarau ya tabbatar da ziyarar ta musamman tare da tattaunawa akan abubuwan da su ka shafi siyasar Jihar Kano.

Kakakin na Shekarau bai yi cikakkiyar bayani ba akan irin abubuwa da aka tattauna a lokacin ziyarar amma majiyoyi sun tabbatar wa Premium Times cewa ziyarar ta su Dangwani tana da alaka da zawarcin Malam Shekarau ya dawo Jam’iyyar PDP a daidai lokacin da maigidansu Kwankwaso yake bankwana da PDP.

Malam Shekarau wanda shi ne sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya yana fama da rikici a Jam’iyyarsa ta APC da kuma Gwamna Abdullahi Ganduje akan jagorancin Jam’iyyar a Kano.

Jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito yadda Kwankwaso yace zai fice daga PDP a karshen wannan watan Maris amma wasu daga cikin hadimansa irinsu Dangwani sun yi masa tutsu sun ce za suyi zamansu a PDP.

Ziyarar Tambuwal

‘Yan siyasar sun kuma ziyaraci gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal duk a cikin shirinsu na samawa kansu makoma a PDP.

Tun da farko Yusuf Dambatta, wanda tsohon kwamishina ne a lokacin mulkin Rabiu Kwankwaso ya wallafa hotunan ziyarar a shafinsa na Facebook a safiyar yau Lahadi.

Bello Ɗambatta, ya ce sun ziyarci Gwamna Aminu Tambuwal ne a cigaba da su ke yi na ziyara tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyya PDP da ke shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya.

“A cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a shiyyar Arewa maso Yamma da ma kasa baki daya, Dr. Yunusa Dangwani, Dr. Yusuf Bello Danbatta, Hon. Abubakar Nuhu Danburan da NW women leader Hajiya Zainab Audu Bako sun ziyarci mai girma Gwamnan Sokoto His Excellency Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal a masaukin gwamnan na garin Abuja”.

Ziyarar ta Tambuwal ta zo da mamaki saboda Kwankwaso ya taɓa zargin gwamna Tambuwal da yin katsalandan cikin al’amuran jam’iyyar PDP a jihar Kano, wanda masana harkokin siyasa ke kallon hakan ne ya tilasta Madugun Kwankwasiyyar ƙoƙarin ficewa daga jami’yyar ta PDP.

Haryanzu Kwankwaso yana cikin Jam’iyyar ta PDP amma wasu magoya bayansa a Karamar Hukumar Rano ta Jihar Kano sun fara ficewa.