Dalilin da ya sa Matawalle ya sallami kwamishinoni da shugabannin hukumomin gwamnatin jihar Zamfara dukan su

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya gama shiri tsaf domin komawa jam’iyyar APC a ranar dimokradiyya, wato 12 ga Yuni.

Majiya mai karfi ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa duk a shirin canja shekar ne matawalle ya yi wancakali da duka kwamishinonin sa da manyan shugabannin hukumomin gwamnatin
Jihar, harda sakataren gwamnati da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.

Majiya ta shaida mana cewa ba an gama shiri tsaf domin canja shekar, sai dai ba a fadi yadda makomar tsohon gwamna zai kasance ba. An ya za su iya zama rumfa daya kuwa a jam’iyya daya, sannan kuma shugabancin jam’iyya doole ta ta shi da ga hannun Abdulaziz ya ri ta koma hannaun gwamna Matawalle.

Matawale ya kori kwamoshinoni sa

A wata sanarwar da ta fito daga ofishin kakakin gwamnan, Bappa Zailani, ranar Talata, gwamna Matawalle ya umarci duka wani shugaban wata hukuma ta gwamnati a jihar ya mika ragamar shugabancin hukumar ga babban darekta a ma’aikatar sa.

Wannan kora bai bar kusan kowa ba domin ya faro ne tun daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnan jihar, zuwa sakataten gwamnatin jihar ya gangara har kwamishinoni sai kuma shugabannin ma’aikatun gwamnatin jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce kwamishina daya ne tal ne kawai ba a wancakalar ba, kwamishin Tsaro da Harkokin cikin gida, Mohammed Tsafe.