Dalilin da ya sa Kwankwaso ya ki amsa gayyatar EFCC bayan matar Ganduje ta ki amsa gayyatar hukumar itama

Jim Kadan bayan fidda labarin kin amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi wa maidakin gwamnan jihar Kano, Hafsat Ganduje, hukumar ta gayyaci tsohon gwamnan jihar kuma tsohon aminin Ganduje, Sanata Rabiu Kwankwaso.

EFCC ta gayyaci Kwankwaso ya bayyana a gabanta domin ya amsa tambayoyin kan wasu harkalla da ake zargin ya aikata a lokacin yana gwamnan kano da suka hada da raba filayen jihar ba tare da an bi ka’ida ba da kuma handame miliyoyin kudin jihar.

An zargi Kwankwaso da rarraba wa abokan sa filaye a lokacin da yake gwamnan jihar.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga Labarin yadda maidakin gwamnan Kano Hafsat Ganduje da dan ta suka kicimi a wata harkallar filaye da ya kai ga hukumar EFCC ta gayyace amma ta ki zuwa.

Dan gwamna Ganduje ya aika wa hukumar EFCC takardar a gayyaci mahaifiyar sa ta yi bayani kan wasu kudaden harkallar filaye da ya bata amma kuma ta lamushe, bata maida musu da kudin su ba, ta yi shiru.