Dalilin ajiye muƙamin Darakta Janar ɗin Kungiyar Gwamnonin APC – Salihu Lukman

Darakta Janar na Ƙungiyar Gwamnonin APC Salihu Lukman ya maida raddi dangane da ce-ce-ku-cen da ake ya yi kan ajiye aiki da ya yi na Daraktan ƙungiyar.

Labarin saukar sa daga aikin ya fara bazuwa ne a ranar Litinin, ba tare da ƙaryatawa daga ɓangaren Lukman ko kungiyar gwamnonin ba.

Sai dai kuma a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, Lukman ya tabbatar da ajiye aikin da ya yi, inda ya ce ya aika wa Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.

A cikin wasiƙar, Lukman bai bayyana dalilan sa na ajiye aiki ba, amma ya ce ya ajiye aiki ne domin ya samu sukunin ci gaba da ragargazar jam’iyyar APC, har sai ya ga ta koma a kan matakin martabar da aka san ta da ita a baya.

Ya ce ya na so ya ga jam’iyyar ta koma kan turbar dalilin kafa ta da muradin da jam’iyyar ke da shi wajen inganta ƙasar nan.

“Na ƙi cewa komai saboda ina jiran amsa daga ƙungiyar gwamnonin. Sannan kuma shugabannin jam’iyya da ‘yan uwa da iyali na sun roƙi kada na ce komai. Kuma su na shaida masu cewa na dauka ne don na yi kamfen ɗin maida APC bisa turba miƙaƙƙa.”

Lukman dai ya yi ƙaurin suna wajen ragargazar tsarin shugabancin APC na ƙasa, ko kuma shugabannin su kan su.

Kafin saukar sa, wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa wasu gwamnoni na ƙoƙarin tsige shi, to amma sai wasu gwamnonin makusantan sa su ka gaggauta ba shi shawarar cewa ya sauka kawai kafin a cire shi.

Lukman tun a baya ya riƙa ragargazar Adams Oshiomole a lokacin da ya ke shugabancin APC.

Hakan ya sa da dama sun riƙa zargin cewa wasu gwamnoni ne ke ɗaure masa gindi ya na sukar tsohon shugaban, domin a cire shi kafin zaɓen 2023.

To haka ta sake faruwa inda a baya-bayan nan ya riƙa zaƙalƙalewa wajen ragargazar shugabancin Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe.