Dakarun tsaro na OPSH ta ceto dagacen Vwang ta kama masu garkuwa da mutane biyu a jihar Filato

Kakakin rundunar tsaro na ‘Operation Safe Haven (OPSH)’ a jihar Filato Ishaku Takwa ya bayyana cewa dakarun sa sun ceto dagacen Vwang dake karamar hukumar Jos ta Kudu Gutt Balak daga hannun masu garkuwa da mutane.

Takwa ya ce rundunar ta kuma kama mutum biyu dake da hannu wajen yin garkuwa da basaraken.

Ya fadi haka ne wa manema labarai a cikin wannan makona garin Jos.

Takwas ya ce an yi garkuwa da Balak ranar Lahadi da dare a hanyarsa ta dawowa garin Vom bayan ya taso daga wani taro da aka yi kusa da ma’aikatar NIPSS dake Kuru a karamar hukumar Jos ta Kudu.

“Bayan rundunar ta samu labarin yin garkuwa da basaraken sai Manjo-Janar Ibrahim Ali ya sa jami’an tsaro a Riyom su fara gudanar da bincike.

” Tare da hadin gwiwar mafarauta, kungiyar ‘yan sakai da sauran jami’an tsaro rundunar ta gudanar da bincike a Sabon Gida-Kanal, Gero da Dahl.

” Jami’an tsaron sun kama wasu mutane biyu a wani kangon gini wanda hakan ya taimaka wajen ceto basaraken daga hannun masu garkuwa da mutane.

Takwa ya ce hakan ya faru ne bayan an yi wata daya da masu garkuwa da mutane suka arce da sarkin Gindiri Charles Dakat.

Yin garkuwa da mutane musamman sarakunan gargajiya na gab da zama ruwan dare a jihar Filato.

Takwa ya yi kira ga mutane da su hada hannu da jami’an tsaro domin kare dukiyoyi da rayukan mutane a jihar.